Tsarin tsagin wata ko murmushin kasa-wani tsarin adana muhalli-Hoto: WWF-Kenya    

Daga Sylvia Chebet

A ranar da manyan biranen duniya suka kashe wutar lantarki na tsawon awa daya domin Bikin Awar Duniya a ranar 23 ga Maris, wasu mata a birnin Amboseli da suke zagaye da manyan dazuka sun yi murnar ce ta wata hanyar daban domin girmama duniya.

Sun haka daruruwan ramuka da suka yi kama da tsagin wata wadanda suke kama da hoton murmushi a cikin Ganjun Dajin Amboseli mai girman gaske, inda yankinsa ya zarce zuwa dutsen Kilimanjaro.

Rijiyoyin da suka haka din suna da wasu amfani daban, suna taimakawa wajen karba da tara ruwan sama, wadanda ba babu su, zai kwarora ne, sannan ya tsane, wanda hakan zai iya jawo zaizayar kasa da ambaliya.

“Yanzu haka an fara ganin alfanun wannan aikin. Mun ga yadda ciyayi suke habaka, wanda hakan ke kara karfafa gwiwar masu gudanar da aikin kasancewar suna ganin sakamako mai kyau cikin kankanin lokaci,” inji manajan dawo da martabar muhalli na Gidauniyar Big Life da ke sa ido a kan aiki, Ernest Lenkoin a zantawarsa ta TRT Afrika.

Wata mazauniyar yankin, Ngameri Maiyo ita ma ta amince da hakan.

“Shanunmu sun samu ciyawa, sannan yanzu wasu dabbobi da dama kamar su jakin daji da barewa har zaki ma suna zuwa wajen nan. Gaskiya mun ji dadin wannan aikin,” in ji ta.

Tsarin tsagin wata ko murmushin kasa-wani tsarin adana muhalli-Hoto: WWF-Kenya

“A da can dabbobin dajin nan barna suke mana sosai a gonaki. Ka ga gwanki ma a lokacin idan muka shuka wake, suna zuwa su cinye. Dole sai dai mu yi shukan tare da wasu hatsin. Gaskiya wannan aikin na saka ni farin ciki sosai,” inji Ngameri.

Ganjun Dajin yana da matukar amfani wajen adana rayuwar dabbobin da suke rayuwa a tsakanin Gandun Dajin Amboseli da na Tsavo. Sannan mutanen garin Maasai suna samun abinci ta hanyar ayyuka a wajen, sannan sukan yi kiwon dabbobinsu a ciki.

Rijiyoyin suna da tsawon mita 2.5 da fadin mita 5. Girman rijiyar na kusa da girman karamin giwa.

An haka su ne a daidai gangara, sannan rufinsu na kallon kasa, wanda hakan ya sa suke samun saukin karba da tara ruwan saman.

Don haka, ba tara ruwan saman kawai suke yi ba, suna taimakawa wajen sanyaya kasa.

Rijiyoyin an tsara su ne domin adana ruwa, da kuma kiyaye zaizayar kasa, sannan sun taimaka wajen gyara kasa ta hanyar dawo da yankunan da suka zaizaye da kuma rage illar sauyin yanayi.

“Sannan kasancewar an yi bakinsu da fadi, sai ya kasance suna iya kara budewa, wanda hakan ke kara yawan ciyayi a wajen,” inji Samuel Jakinda, manajar shirin ‘Just Dig It’, sannan ya kara da cewa aikin ya taimaka wajen adana muhalli da saukaka illar sauyin yanayi kuma yana taimakon mutane.

Matan yankin na Amboseli sun yi bikin Ranar Ban-Kada ne  - Photo: WWF-Kenya

Women at Work

“Muna amfani da rijiyoyin nan ne domin kiyaye illar sauyin yanayi kasancewar yankin yana fuskantar barazanar zaizaiya, wadda ke karuwa a sanadiyar lalacewar tsarin kiwon yankin,” inji Dokta John Kiko, kodinetan asusun adana yanayi na duniya wato World Wide Fund for Nature (WWF-K) a yankin Amboseli.

“Don haka, akwai bukatar mu dawo da tsarin adana dabbobinmu, sannan yadda wannan tsarin ke taimakawa shi ne yana zama wata matattara ce, wadda a karshe take taka rawa wajen gyara kasa,” in ji shi.

Shirye-shiryen da asusun WWF-K ke daukar nauyi irinsu Just Dig It da Big Life da Gidauniyar Big Life sun fara gudanar da ayyukansu ne a shekarar 2021 domin wayar da kan mutane a kan magance sauyin yanayi.

“Zuwa yanzu mun gyara hekta 10,000 a ayyukanmu daban-daban, sannan abin da muka fahimta yanzu shi ne tun a shekarar 2021 muke samun sakamako masu kyau,” in ji Kioko na WWF-K.

Yankin suna ganin cigaba a bangaren adana dabbobin yankin kamar kwari da tsuntsaye da wasu dabbobin da kuma sauya yanayin wurin zuwa kore. Wannan ya kara karfafa gwiwar matan domin su cigaba da aikin haka rijiyoyin.

“Mu kusan kullum muke bikin Awar Duniya. Duk safiya muke zuwa wannan waje muna aiki. Ni kadai nakan haka ramuka guda shida tsakanin 7:30 na safe zuwa 2 na rana. Idan dukkanmu mu 120 kowa na haka guda shida a kullum, za a samu ramukan da dama,” in ji Valentine Semeya.

“Akwai bukatar mu hada karfi da karfe domin dawo da martabar dazukanmu da dabbobinmu da muhallinmu,” inji Jakinda.

Mata a bakin aiki

“Jagororin shirin duk mata ne. Kuma muna sane muka tsara hakan domin mun gano cewa sauyin yanayi ya fi shafar mata duk da cewa ba su cika fitowa fili suna korafi ba.”

Wani mazaunin yankin Sketa Imelaisa, ya yi amannar cewa aikin yana da matukar amfani.

“Wani lokacin farin da ake yi yakan ba mu wahala. Muna da dabbobi amma sai ya kasance babu wajen kiwo, amma nan da wasu shekaru, muna da yakinin wadannan ciyayin za su taimaki mutanen Maasai,” inji Imelaisa.

“A lokacin rani, mukan saya ciyayi ne. Idan ba ka da kudi, kakan ji kamar ka yi sata saboda dole dabbobinka suna bukatar ciyawa, amma kuma ba ka da kudin da za ka saya domin ka ciyar da su,” in ji Purity.

“Idan shanu suka zo nan, suna ci su koshi, wanda dah akan mu kuma muke samun madara sosai. Da madarar muke samun kudin da muke ayyukan kungiyarmu, sannan mu dauki nauyin karatun yaranmu.”

TRT Afrika