Helen Adebayo da mijinta sun mallaki karnuka Rottweilers guda 13 waɗanda suka kasance tamkar dangi da abokai a ciki iyalinsu.

Daga Pauline Odhiambo

12 ga watan Mayu na 2013, rana ce da ba za ta taɓa gushewa daga tunanin Olaolu Adebayo ba, Olaolu yana gida yana shirin zuwa coci tare da matarsa da dansa sai ya ji an dora masa bindiga a kansa.

“Da misalin karfe 9 na safe ne, adaidai lokacin ina jiran matata a cikin motarmu a wajen kofar gidan, sai na ji an ɗora min bindiga a kai, kuma aka umarce ni da in fita na koma cikin gidanmu,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

"Ɗana yana ɗan watanni shida kacal a lokacin."

Sakamakon firgita da lamarin, matasan ma’auratan suka yanke shawarar ƙaura zuwa wata unguwa mafi aminci a jihar Ondo da ke yankin kudu maso yammacin Nijeriya.

Amma da aka sake yunkurin yin fashi da makami a wani gida da ke kusa da su, sai suka yanke shawarar samo kare da zai na gadinsu.

Rottweiler suna cikin nau'ikan karnuka masu fada da zafin nama.

''Karnuka masu ban tsoro''

"Mun yi wani bincike kuma mun gano cewa nau'ikan karnuka Rottweilers suna da kyau sosai wajen gadi, kuma mutane da dama suna jin tsoronsu saboda girmansu," in ji Helen Adebayo.

Asalin karnukan ana kiwonsu ne don aikace-aikace, galibi akan yi amfani da nau'in Rottweiler wajen kiwon dabbobi.

A yanzu haka dai sun fi shahara ga ayyukan yan sanda, wajen taimaka wa bincike da ceto har ma a matsayin karnuka da ke jagora ga masu fama da nakasa.

Nauyin babbar macen Rottweiler na iya kaiwa kilo 48 yayin da maza kuma kan iya kai kilo 60 sannan tsayinsu zai iya kaiwa inci 27.

Rottweilers ko Rotties kamar yadda ake kiran su, suna da girma sosai ko a ƴan kwikwiyonsu kana suna girma su zama masu samar da kariya - tasirin da ya kara yawan buƙatun su a matsayin karnuka masu gadi.

Adebayos sun zaɓi ɗan kwikwiyon karen da suka sawa suna 'Spartan' - sunan da da ya samo asali daga ɗaya daga cikin fina-finan da Olaolu ya fi so game da bataliyar jarumai mara tsoro da ke kare yankinsu daga mahara.

Kamar dai sunansa, Spartan's ya riƙa ya kuma yi girmar da har ya kusan wuce mai renonsa a tsayi a cikin tsawon shekara guda da haihuwarsa kuma yana tsoratar da masu kokarin kai kutse da girman jikinsa.

"Mutane ba sa son zuwa kusa da gidanmu bayan mun sami Spartan," in ji Olaolu wanda ke shafe lokaci yana aiki a matsayin likitan fiɗa a wani asibiti

"Akwai dalibai da dama da mu ke zama a unguwa daya da su, don haka ko bata gari daga cikinsu basa gangancin zuwa kusa da mu saboda Rottweiler," in ji Olaolu.

Daga nan Maƙwabta suka soma tambayar ma'auratan game da nau'in karen Spartan, da kuma yadda za su mallaki irinsa.

La'akari da cewa ma'aurantan dukkansu sun girma a gidan da akwai karnuka, Helen da Olaolu sun ba wa maƙwabtansu duk bayanan da suka sani game da kiwon nau'in kare Rottweilers da sauran nau'ikan karnuka, da kuma kudaɗen da za a kashe wajen kula da su.

Rottweiler mace mai koshin lafiya na iya haifar tsakanin ƴan kwikwiyon karnuka tsakanin shida zuwa 12.

''Tsantsar nau'in Rottweiler''

"Muna kashe makudan kudade wajen kula da Spartan, don haka muka fara neman hanyoyin samun macen Rottweiler don ta hayayyafa don mu iya sayar da ƴan kwikwiyonta mu samu karin kudaɗɗen shiga," in ji Helen.

Farashin ɗan kwikwiyon karen na kaiwa dala 450 a Nijeriya, adadin da ke da tsada a kasar da aka kiyasta tana da karnuka kusan miliyan 10, sai dai yawancin irinsu ba su da yawa, kamar yadda bayanai daga PetLovers Nigeria suka nuna.

Kashi 33 cikin 100 na al'ummar ƙasar ne suka mallaki karnuka, kana kiwon karnuka na ɗaɗa bunkasa zuwa kasuwancin da ke iya samar da riba.

A lokacin da aka fara haɗa Spartan da macen Rottweiler mai lafiya, an haifi ƴan kwikwiyon guda takwas daga gwajin kiwon da aka soma.

Sai gashi abin da aka soma a matsayin hanyar samun kuɗin kula da Spartan sannu a hankali ya bunƙasa zuwa wani kamfanin kiwon nau'in karen mai suna Onyx and Jewel Rottweiler Breeders - kasuwancin da ya zuwa yanzu ya fitar da nau'ikan karnukan Rottweilers 150.

Nau'in zuriyar Rottweiler sune wadanda iyaye iri ɗaya suka haife su - '' tsantsan nau'i iri ɗaya'' galibi a ka'idojin kamfanin Onyx and Jewel suna ƙarban karnuka ne don kiwonsu daga wasu manyan wuraren da ake haifar a ƙasar.

"Yana da mahimmanci a tabbatar da cewa karnukan da aka haɗa su barbara, lafiyayyu ne, kuma am musu dukkan allurar riga-kafin da suka kamata. sannan dole ne a ciyar da su da kyau kuma a aije su a tsaftataccen wuri masu dumi don guje wa kowace irin cuta ko kamuwa da wata cuta,'' in ji Helen.

"Da zarar macen karen ta samu juna biyu, mu kan ci gaba da ba ta abinci mai gina jiki wanda ya ƙunshi madara da kwai da niƙanan kaji, sannan muna ƙara wa da sanadaran cin abinci na multivitamin a makonni tara na ciki.."

Olaolu da Helen Adebayo sun fito daga dangin da suka mallaki karnuka. 

Ciyarwar kwalba da alluran riga-kafi

Mace mai lafiya za ta iya samun zuriyar ƴan kwikwiyon karnuka shida zuwa 12. Ana tsaftace ƴanƴan nana da nan bayan an haife su kuma a ajiye su a cikin ɗaki mai dumi tare da uwayen su don su samu damar nshayar da su.

"A wasu lokuta dole ne mu ciyar da ƴan kwikwiyon da kwalba musamman idan sun yi yawar da da ba za a iya shayar da su sosai da nonon uwa ba," in ji Olaolu.

"Da zarar sun cika wasu ƴan makonni, muna ba su maganin DHLPP wanda wani nau'in maganin riga-kafi ne da ke kare su daga cututtuka daban-daban." in ji shi.

Ana kuma kiran maganin da Canine Distemper, DHLPP yana kare karnuka daga kamuwa da cutar makanta ta distemper da cututtukan parvovirus da parainfluenza da nau'i biyu na cutar adenovirus canine (hepatitis).

"Bayan kusan makonni shida da haihuwa, muna raba su da uwayensu ta yadda za su iya fara dandana rayuwa da dogaro da kansu, za su iya zuwa sabbin muhallinsu ko iyalansu a makonni takwas," a cewar Olaolu, yana mai kari da cewa sakewa cikin rana yana da kyau ga ƴan kwikwiyon don ƙasusuwansu ya yi karfi.

Kamfanin Onyx yana taimakawa sabbin mutanen da suka mallaki karnukan tuni da lokutan da ya kamata a yi musu allurar riga-kafi.

Warkar da Karnuka

Rottweilers suna da matsakaicin tsawon rayuwa na shekaru 10 kuma a shakara uku girman jikinsu ke gama cika.

“Mu cikakkun mambobi ne na kungiyar Rottweiler Breeders Society a Nijeriya kuma kamfaninmu ma yana daga cikin kungiyar masu kiwon nau'in Karnuka iri daban-daban; don haka duk karnukan mu suna da cikakken bayanan zuriyar da suka fito a cikin rajista,” in ji Olaolu.

Yawancin abokan cinikin kamfanin Onyx suna samun Rottweilers ne saboda dalilai na tsaro amma wasu da dama suna daraja su ne kawai don abokantaka da kusanci yanayin da Olaolu ya tabbatar.

“A yanzu haka iyalina sun mallaki Rottweilers guda 13 ciki har da yaronmu 'Spartan' Sun kasance muhimman abokai a gare mu da ’ya’yanmu hudu,” in ji shi.

"Lokacin da na dawo gida daga aiki, karnukan su kan yi tsalle a kaina tare da nuna farin cikinsu kuma nan da nan sai na ji duk gajiya da damuwa da na kwaso daga wajen aiki sun tafi."

TRT Afrika