Daga Yahya Habil
Yayin da adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kaiw Zirin Gaza, da kuma yadda duniya ke ci gaba da shaida yadda ake cin zarafin Falasdinawa, ya kamata 'yan Afirka su tsaya su yi tunani a kan abin da lamarin Falasdinawa ke nufi a gare su.
Kasashen Afirka da dama sun nuna juyayi da goyon baya ga al'ummar Falasdinu.
Hasali ma, ƙasashen Afirka sun kasance ƙashin bayan ƙudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 3379, wanda ya ayyana aƙidar kafa ƙasar Isra'ila a matsayin wani nau'i na wariyar launin fata da nuna ƙyama.
Kazalika, ga wasu 'yan Afirka, su ɗauki lamarin Falasdinawa da muhimmanci ba sosai. Suna ganin rikicin Isra'ila da Falasdinu bai shafi Afirka da 'yan Afirka ba kai tsaye. Hakan na iya yiwuwa saboda dalilai na bambancin yanki da kuma ra'ayinsu na cewa batun Falasdinu 'fafutuka ce ta Larabawa'.
Yana da kyau a fahimci cewa al'amarin Falasdinu ba wai kawai na Larabawa ba ne - abu ne da ya shafi dukkan ɗan'adam.

Kamar yadda kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 3379 ya bayyana, salon da Isra'ila ke bi na nuna wariya ya za ta zama ƙasamai wariyar launin fata, wani abu da 'yan Afirka suka saba da shi.
Gwamnatin Isra'ila ta yanzu tana aiwatar da al'amura na nuna wariyar launin fata irin wanda ya faru a Afirka ta Kudu, inda wariyar launin fata ta zama ita ce dokar ƙasa a baya.
Daidaita hakkoki
Hakan ya ƙara samun goyon bayan kalaman jami'ar diflomasiyyar Afirka ta Kudu Nalendi Pandor a watan Yulin 2022, sama da shekara guda kafin a fara yaƙin da ake yi a yanzu na Isra'ila da Gaza, inda ta ce "labarin gwagwarmayar al'ummar Falasdinu ya tunowa mutanen Afirka ta Kudu nasu tarihin na wariyar launin fata da zalunci da suka fuskanta."
Gwamnatin Afirka ta Kudu baki daya ta fahimci hakan da kyau, don haka ne a ko da yaushe Afirka ta Kudu ke nuna goyon bayanta ga Falasdinu.
Kasar ta yi Allah wadai da hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza, har ma ta shigar da ƙorafi kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke Hague, inda ta buƙaci a gudanar da bincike kan ayyukan da Isra'ila na baya-bayan nan, wanda shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya kira da ''kisan ƙare dangi'' da '' laifukan yaƙi ''.
Abubuwan da Afirka ta Kudu ta yi a baya-bayan nan sun nuna cewa a haƙiƙa akwai gagarumin sauyi ga sabon ra'ayi na gama gari da aka ambata.
Ana ƙara rarraba sanya Isra'ila a jerin ƙasashen da suka yi mulkin mallaka irin su Faransa da Biritaniya, tare da gwamnatocin wariyar launin fata irin su rusasshiyar gwamnatin mulkin wariyar launin fata ta Afirka ta Kudu.

Bayan haka, hakan yana ƙara zaburar da mutane musamma kasancewar ɗaya daga cikin manyan ƙasashe masu tattalin arzikin nahiyar wacce kuma ta taɓa faskantar wariyar launin fata ta ɗauki irin wannan matsayi.
Tashi tsaye don yaƙar zalunci
Kuma kamar yadda zamanin mulkin wariyar launin fata ya ƙare a Afirka ta Kudu tare da kafa kasar da ta bai wa farare da bakaken fata 'yan Afirka ta Kudu hakkokinsu daidai-wa-daida, ana iya, kuma ya kamata a kawar da wariya a Isra'ila.
Ya kamata 'yan Afirka su ci gaba da yin kira da a samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu da za su samar da daidaito ga Falasdinawa da 'yan Isra'ila.
A takaice dai, ya kamata 'yan Afirka su kula da darussan abubuwan da nahiyarsu ta fuskanta a baya.
Darussan da aka koya daga ta’addancin ‘yan mulkin mallaka da kuma zaluncin ‘yan Afirka zai kasance a banza idan ‘yan Afirka a yau ba su tashi tsaye wajen yaƙar duk wani nau’in zalunci ba a duniya.
Marubucin, Yahya Habil, ɗan jarida ne mai zaman kansa a Libya da ke mayar da hankali kan harkokin Afirka. A yanzu yana aiki ne da wata ƙungiyar bincike a Gabas ta Tsakiya.
Togaciya: Ba dole ba ne ra’ayin marubucin ya zo daidaida ra’ayi ko ka’idojin aikin jaridar TRT Afrika.