Na'urorin kakkabo makamai masu linzami na Isra'ila bayan Iran ta aika da jirage marasa matuka da makamai masu linzami zuwa kasar, kamar yadda aka gani a Ashkelon a 14 fa Afrilun 2024. Hoto: Reuters      

Daga Imran Khalid

A wani sabon yanayi daban, yankin Gabas ta Tsakiya ya sake faɗawa cikin tashin hankali da fargaba bayan jirage marasa matuka da makamai masu linzami na Iran suka fara shawagi a sararin samaniyar yankin.

Hare-haren, ramakon gayya ne a kan harin da Isra'ila ta kai a Ofishin Jakadancin Iran da ke Syria, wanda hakan ya sa Iran ta fito fili ta fara yaƙin, maimakon na sari-ka-noƙe.

Maimakon cigaba da yaƙin bayan fage, wannan karon Iran ta fuskanci Isra'ila kai tsaye, matakin da a lokaci ɗaya yake ba da mamaki, sannan yake nuna kamar takala ce a fili.

Amma duk da haka, a karkashin kasa, hare-haren sun fi kama da fargar jaji.

Bayan harin na Isra'ila a Syria, wanda ya yi sanadiyar mutuwar wasu kwamandojin Iran guda bakwai, ciki har da Birgediya Janar Mohammed Reza Zahedi, martanin da Iran ke mayarwa sun fi kama da nuna ƙarfin soji, sama da neman yaƙi ya ɓarke.

Jawabin Iran ga Majalisar Dinkin Duniya bayan hare-haren martanin da ke nuna cewa "an kawo ƙarshen yaƙin", da kuma buɗe sararin samaniyar ƙasashe masu maƙwabtaka da ita, sun nuna cewa Iran na nuna ƙarfin ikonta ne, ba wai gwabza dogon yaƙi take so ba.

Sai dai duk da haka, yadda Iran ta nuna isarta ya sa masu ra'ayin riƙau na Isra'ila suna kira da ita ma ta sake mayar da martani mai zafi.

Duk da cewa Isra'ila ta sha alwashin mayar da martani ga Iran, har yanzu babu wanda ya san shirinta.

Maimakon fito na fito wajen mayar da martani- saboda rashin samun goyon bayan Amurka da wasu kasashen Turawa, wadanda ba sa so yaki ya mamaye yankin na Larabawa a daidai lokacin da ake cigaba da gwabza yaki a Ukraine - Isra'ila za ta iya komawa yakin sunkuru ta bayan fage da Iran tare da rage fito na fito.

Yaƙin sunƙuru ya fi sauƙi, wanda hakan zai ba Isra'ila damar cigaba da cin dunduniyar Iran ba tare da fito na fito ba.

Duk da cewa Biden ya tabbatar da goyon bayan gwamantinsa ga Isra'ila, alamu sun bayyana ba shi da niyyar shiga yakin dumu-dumu.

Wannan ne ya sa Isra'ila a tsaka mai wuya, saboda dole ta daidaita burinta na mayar da martani, da kuma tunanin yadda za ta yi ba tare da fadada yakin ba.

Haka kuma Iran ta daga farin tuta, wanda ke nuna an gama yaki. "Za a iya cewa an kawo karshen wannan batu yanzu," kamar yadda wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana a kafar X.

Wannan ya kara bayyana yadda lamarin Gabas ta Tsakiya ke da sarkakiya, wanda hakan ya sa yakin fito na fito ke bukatar lissafi sosai.

Gwargwarmayar samun ƙarfin iko

A irin wannan yanayi da yankin ke ciki, duk wani yunkuri yana da tasiri. Wannan tata-burzar tsakanin Iran da Isra'ila ta sake bude wani babi ne na dadaddiyar jikakkiya da ke tsakanin kasashen biyu.

Wadannan hare-haren na kwanan nan, duk a zahiri suna nuni ne da rikicin yankin da kuma alaka da yakin da ake cigaba da gwabzawa a Gaza, amma asalin musabbabinsa shi ne fafutikar nuna karfin iko a yankin na Gabas ta Tsakiya.

A tsakiyar kuma akwai dadaddiyar fafutikar nuna karfin iko, inda Iran da Isra'ila ke fafutikar samun karfin fada a ji a yankin. Sai dai sun hadu a abu daya ba tare da shiri ba, inda suke adawa da samun karfin fada a na Larabawa, musamman ganin yadda suka hada kai a mamayar Amurka a Iraqi ta shekarar 2003.

Wannan 'yar haduwar da suka yi, ta kawo sauyin tunani a yankin, wanda ya sa Isra'ila ta samu karfin iko sosai, sannan ita ma Iran ta samu iko da Bagadaza. Sai dai kuma 'yar alakar ce ta bude wani sabon babi na sabani a tsakaninsu.

A wajen Isra'ila, cigaba da zama daya tilo mai makamin nukiliya a yankin shi ne a gabanta, inda ta kuduri aniyar yin duk mai yiwuwa wajen kawo wa Iran tsaiko wajen mallakar makamin. A bangaren Iran, ita kuma tana ganin mallakar makamin na nukiliya zai daga darajarta.

A daidai lokacin da ake cigaba da dardar a yankin, sannan jiragen yaki suke cigaba da shawagi a sararin samaniya, yankin na Gabas ta Tsakiya na tsaka mai wuya, inda fafutikar samun karfin fada a ji ke neman jefa yankin cikin bala'i.

A wannan gwargwarmayar samun karfin ikon, babu kasar da za ta yi fatar samun matsalar. Ita dai Iran babban burinta shi ne adana shirinta na nukiliya.

Wannan ya sa, duk da jefa makamai masu linzami da Iran ta yi, tana lura da matsalar da yakin fito na fito da Isra'ila zai iya haifarwa, wanda hakan ya sa take bi sannu a hankali. Iran ta yi haka ne domin hana asarar rayukan fararen hula da na sojoji wajen kaucewa fito na fito da Isra'ila, wanda zai iya fadada yakin.

Yunkurinta na adana shirinta na nukiliya ya nuna abin da ya sa take lissafin abubuwan da za ta yi, da ba za su tayar da zaune tsaye ba.

Haka kuma Iran tana lissafin da ya kamata ta yi a bangaren diflomasiyya a duniya, kasancewar ta fara tattaunawa da gwamantin Shugaban Kasar Amurka Joe Biden.

Yiwuwar komawa ga yarjejeniyar nukiliya ta 2015 ya ta'allaka matuka ga yanayin zaman lafiya a yankin, domin duk wani tashin hankali a yankin a yanzu zai iya komar da hannun agogo baya a tattaunawar diflomasiyyar yankin.

Duba da wadannan matsalolin masu daure kai, Iran tana tsaka mai wuya kasancewar barazanar Amurka na taimakon kawarta Isra'ila a kowane lokaci. Wannan ya kara dagula lissafin Iran.

Duk da karfin da Iran ke nunawa, a wani bangaren kuma tana tunanin matsalar da yakin da Isra'ila da Amurka a hade zai haifar mata.

Wannan ya sa take sara tana duba bakin gatari. Gwamantin na Iran ta fahimci kalubalen da take fuskanta na yaki babba a daidai lokacin da Gwamantin Biden ke kara jan kunnenta.

Haka kuma, lissafin Iran ya ma wuce batun karfin soji kawai, tana kuma la'aikari da yanayin yankin nasu na Gabas ta Tsakiya.

Lura da inda ra'ayin kasashen duniya ya koma, musamman game da yakin Isra'ila a Gaza, ya kara nuna dole Iran ta kara lissafi da kyau domin gujewa samun matsala da masu tausaya mata.

Don haka, duk abin da Iran za ta yi, tana yi ne tana duba yadda zai amfanar kasarta.

A yankin da yake yawan fama da tashin-tashina da rashin tabbas, bin abubuwa a tsanake yana da matukar muhimmanci ga masu wuka da nama a Iran. Hare-haren na Iran na kwanan nan ya nuna akwai sarkakiya matuka na fafutikar samun karfin fada a da nuna karfin iko.

Da Rasha da China, duk da suna bin lamarin a hankali, suma sun aika wa Iran da wani sako mai muhimmanci: matsalolin da yakin zai haifar ya fi amfaninsa yawa.

Duba zuwa tattalin arzikin kasashen biyu, da tsare-tsarensu, shi ya sa kasashen biyu suke bin lamarin a hankali domin gujewa rincabewar yaki tsakanin Iran da Isra'ila. Babban burin kowace daga cikinsu shi ne kare martabarta a yankin Gabas ta Tsakiya.

Yadda suka ki amincewa da biye wa mazuga na nuna yadda suka muhinmantar da tattalin arzikinsu da matsayinsu a yankin.

Duk da haka, duk da sabanin bukatu da rarrabuwar ra'ayin kasashen kawance, a bayan fage kuma ana kada gangar yaki, wanda yake kara ta'azzara yanayin rashin tabbas a yankin na Gabas ta Tsakiya. Amma dai a irin yanayi da ake ciki na tsaka mai wuya, babu kasar da za ta so ta yi wani kuskure komai kankantarsa.

Imran Khalid mai sharhi ne daga birnin Karachi a kan al'amuran siyasa. Manyan kafafen watsa labarai na duniya na yawan wallafa maƙalolinsa.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyanana ba sa wakiltar ra'ayi, fahimta, ko manufofin Editocin TRT Afrika.

TRT World