Ana fitar da mafi yawan lu'u-lu'un Namibia zuwa Isra'ila. Hoto: AP Archive

Namibia, kasar Afirka ce 'yar karama, kuma ta bi sahun kasashe da dama da suka bukaci Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya da ta amince da ta'annatin Isra'ila a Gaza a matsayin kisan kiyashi.

Kasar ta Afirka ta Kudu ta yi yunkurin kira da a saka takunkumai ga kamfanonin Isra'ila. Amma wannan ya sanya an mayar da hankula kan kasuwancin lu'u-lu'u na sirri da ke tsakanin Nabia da Isra'ila, wand ahakan ke kawo tambayar ko wannan kira zai kawo wani sauki ga Falasdinawan gaza.

"Abokin kowa, ba ya gaba da kowa," ne falsafar da Namibia ta ce manufofinta na kasashen wake na tafiya a kai, wanda aka assasa bayan kasar ta samu 'yancin kanta daga Afirka ta Kudu a 1990.

A wasu matakai, yarjejeniyar Isra'ila da Namibiata sha fuskantar rashin gaskiya inda Isra'ila ta kasance daya daga kasashen da suka ci gaba da gudanar da kasuwanci da gwamnatin 'yan wariyar launin fata ta Afirka Kudu.

Duk da wannan tarihi, kasashen biyu sun kulla kasuwanci tsawon shekaru. Kuma lu'u-lu'un Namibia ne babban jigon kasuwancin.

Kira ga adalci

A jawabin da ta yi a gaban Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya a ranar 24 ga Fabrairu, Ministar Shari'a ta Namibia Yvonne Dausab ta kwatanta mamayar da Isra'ila ke yi wa yankunan Falasdinawa da gwagwarmayar da Namibia ta yi do kwatar kanta daga hannun 'yan nuna wariya na Afirka ta Kudu, da kuma kisan kiyashi kan jama'ar Nama da Ovaherero da Jamus ta yi a farkon karni na 20.

A yayin zaman kotun, wakilin Namibia Phoebe Okowa, ya bayar da shawarar daukar matakan ladabtarwa kan isra'ila saboda kashe rayuwa, kwace gidaje da filaye da kisan kiyashi ga al'umar Falasdinawa.

Okowa ya kuma yi kira ga wasu kasashen da su yanke huldar kasuwanci da Isra'ila.

"Dukkan kasashe na karkashin wajabcin kin amincewa, taimakawa ko bayar da gudunmowa ga ci gaba da mamaya ba bisa ka'ida ba, wanda ya hada da wajabcin sauran kasashe a rukuni na uku kar su taimaka ta kowacce fuska ga Isra'ila."

A lokacin da Namibia a fakaice ta yi kira da a kaurace wa Isra'ila, an dinga tambaya game da alakar kasuwanci da ke tsakanin Namibia da Isra'ila wadda ita ce ta fi amfana da danyen lu'u-lu'in da kasar ke fitarwa.

A bayyane take karara Namibia za ta kafa abin misali wajen saka wa wadannan kasuwanci takunkumi.

Yaya batun lu'u-lu'u?

Daraktan Zartarwa a Ma'aikatar Ma'adanai da Makamashi, Penda Ithindi ta ce yanayin zuba jarin Isra'ila a Namibia ba zai zama kebantaccen abu duba da kasarsu ba, takunkuman tattalin arzikin da za a saka wa Isra'ila ba zai yiwu a karkashin dokokin Namibia ba.

"Namibia na huldar kasuwanci da kulla alaka a matakin kasa da kasa," ta fada wa TRT World.

"Sakamakon haka, Namibia ba ta hada kanta da matakan da kasashe tilo suka dauka don warware wata matsala ta duniya. Dukkan zuba jari a kasar na kasnacewa ne a karkashin dokar da ake da ita ta manufofin kasuwanci."

A 2022, Namibia ta fitar da kaya na dala miliyan $59.82 na kayayyaki zuwa Isra'ila. Sun sayi kayayyaki na dala $3.8 daga Isra'ila, mafi yawan kayan injina yankawa da goge lu'u-lu'u.

Isra'ila ta fuskanci matsin lamba a lokacin da kasashe da dama da suka hada da Namibia sun bukaci ICJ da ta bayyana abin da ke faru wa a Gaza a matsayin kisan kiyashi. Hoto: AP archive

Duk da cewar shugabannin Namibia na goyon falasdinawa, amma da wahala su iya hakura da kasuwancinsu da suke yi.

Lu'u-lu'u ne abin da ya fi kawo wa Nabia kudaden shiga.

Wani bincike da duba takardun kamfanonin da ke kasuwanci a Hukumar Kula da Kamfanoni da Kasuwanci ta Namibia, ya bayyana an yi wa mafi yawancinsu rejista a Isra'ila.

Tuliameni Kalomoh, tsohon Mataimakin Ministan Harkokin Waje, ya yi gargadi da cewa kalaman Namibia a ICJ na iya kawo tambayar sahihancinta duba da alakar kasuwanci da ke tsakanin kasashen biyu.

"A lokacin da kake magana da bakunanka, za ka iya janyo cece-ku-ce game da dattijantakarka. Wani a iya tunanin wannan kalami kamar irin wanda Ministar Shari'a ta yi a ICJ, ya kamata a ce an sake duba shi da tsara shi a karkashin ma'aikatar Harkokin Waje wadda ita ke da wannan alhaki."

"A duk lokacin da kasa ta yi kira ko bayar da shawarar saka takunkumi kamar yadda Namibia ta yi, dole ne a kalli irin tasirin da wannan takunkumi zai janyo, kuma a irin wannan yanayi zai cutar da Namibia ne maimakon amfanar ta," Kalomoh ta fada wa TRT Hausa.

Kuskure ne wannan kalami na Ministar Shari'a kan batun diplomasiyyar kasa da kasa, a lokacin da ake da hukumar da ke da alhakin yin hakan, in ji Kolomoh.

A ce Namibia ta yi wannan kira na kasa da kasa kan a saka wa Isra'ila takunkumai, amma kuma ba ta da niyyar yanke huldar kasuwanci da ita, to za a yi ta tambaya game da inganci da gaskiyar wannan kira, in ji Kalomoh.

Babbar alaka

Lev Leviev, Julius Klein, da Maurice Tempelsmann manyan masu kasuwancin lu'u-lu'u ne a matakin kasa da kasa kuma sun mayar da hankalin kan na kasar Namibia.

Kamfanonin Lev Leviev Diamonds, Julius Klein Diamonds, da Kaplan Lazar na gudanar da aikinsu tare da kamfanin Namibia Diamond Trading Company (NDTC) inda suka dauki dubunnan ma'aikata a Namibia a kamfanonin da suke yanka wa da wanke lu'u-lu'u.

Su ne kuma aka sani da abokan huldar NDTC, wanda shi ne kamfanin gwamnati na Namibia d ake d alhakin sayen sayar da danyen lu'u-lu'u don yankawa da wanke shi a Namibia.

Lev leviev da kamfaninsa sun zama karkashin sanya idanun kasashen duniya a lokaci da wani rukuni na Falasdinawa ya kai su kara yana neman dala biliyan $34, bisa zargin ya amfanar da wuraren da yahudawa suka kwace wa Falasdinawa a Yammacin Gabar Kogin Jordan.

Wani rahoto da wata cibiyar aikin jarida ta fitar ya bayyana yadda masana'antun sarrafa lu'u-lu'u suke da hannu wajen mamayar yankunan Falasdinawa.

"Karar da aka shigar a Washington DC ta yi zargin an aikata laifuka da dama karkashin dokokin Amurka da dokokin kasa da kasa, ciki har da kisan kiyashi, laifukan yaki, da keta hakkokin dan adam, kulle-kulle, satar kudaden gwamnati, rashawa, bata suna da kage" Ntibinyane Ntibinyane ya rubuta a wata makala.

Baya ga kasuwancin lu'u-lu'u, kamfanin kayan soji na Namibia da wani kamfanin Isra'ila FK Generators and Equipment na aiki tare don gina wata cibiyar samar da makamashi 'Anixe' a garin Walvis Bay na gabar teku.

Kamfanin samar d alantarki na Namibia NAMPOWER ya dauki hayar kamfanin FK Generators don samar da ma'ajiyar mai ta kasa ta hanyar hada gwiwa da kamfanin sojin Namibia.

Kira ga saka takunkumi ga kamfanoni masu zaman kansu na Isrra'ila na iya zama makararren mataki.

Amma hadin kan soji tsakanin Isra'ila da gwamnatin Namibia ya fado ne cikin iyakokin kalaman da Namibia ta yi a gaban kotu a Hague na cewa "dukkan kasashe na karkashin wajabcin tabbatar da ba su bayar da dama ga kamfanonin kasashensu sun yi hulda da dukkan kamfanonin Isra'la da suke da hannu a mamaya ba."

Wannan na kawo tambayar ta yaya Namibia ta nemi a matakin kasa da kasa a kaurace wa kamfanonin Isra'ila amma kuma a cikin gidanta ba a yi hakan ba, shin sauran kasashe za su dauke ta da muhimmanci?

Vitalio Angula dan jarida ne da ke Windhoek Namibia. @vita_angula

Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya zama daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.

TRT Afrika