Ana ganin ma'adinin Uranium na Tamgak a cibiyar hakar uranium ta Areva ta Somair a Arlit, Nijar. Hoto: Reuters Archive      

Daga Mahaman Laouan Gaya

Rikicin jari-hujja da ya dabaibaye kasashen Yammacin Turai ya kara jawo hankalin kasashen zuwa ga albarkatun ma’adinan da suke jibge a karkashin kasashen Afirka, musamman wadanda ke yankin Sahel da aka fi sani da "iyakoki uku".

Idan ana maganar albarkatun kasa, (ma’adinai da fetur da gas) a yankin Sahel na Afrika, a gefe daya ana nufin gano wuraren da suke da wadannan albarkatun ne da kuma tattalin arzikinsu, sannan a daya gefen kuma ana zance ne na yadda za a yi amfani da siyasa da wasu dabarun domin cin moriyar arzikin.

Lallai, ta hanyar amfani da ayyukan jin kai ko tallafin yaki da masu tada kayar baya, yankinmu ya zama wani abin farauta daga kasashen waje a shekara goma da suka gabata ta hanyoyi daban-daban, musamman ta hanyar amfani da agajin soji a wuraren da suke da arzikin albarkatun kasa da makamashi.

An fara dabbaka wannan tsarin ne a kasar Libya, (kisar gillar tsohon Shugaban Kasar Libya, Muammar Gaddafi da kuma rikice-rikicen da suka biyo baya) a shekarar 2011 karkashin jagorancin Faransa da sunan agajin sojin NATO.

A bayyane yake cewa tallafin jiragen na Faransa a kasar, ba an yi su da nufin kare mutanen kasar ba ne, ko kuma da nufin wanzar da dimokuradiyya, sai dai domin kamfanonin kasashen waje su samu damar mallakar ma’adinan kasar ta Libya da makamashinta. Wannan yunkurin, wanda ya ci Libya, ya cigaba da fadada, har ya kai ga yankin Sahel, da ma wasu kasashen Yammacin Afirka.

Jawo rigima da gangan?

Tun wancan lokacin, yankin Yammacin Afrika bai sake samun zaman lafiya ba; juyin mulki a Mali da Guinea da Burkina Faso, da rashin tsaro da yunkurin raba kasar Mali da rashin tsaro a Nijar da Burkina Faso.

Matsalolin rashin tsaron kara ta’azzara suke yi a yankin, sannan suna kara fadada zuwa wasu kasashen irin su Benin da Côte d'Ivoire da Togo.

Wadannan rikice-rikice a Yammacin Afirka, tare da yakin Rasha da Ukraine (wanda ya kawo cikas a hada-hadar gas zuwa Yammacin Turai daga Rasha), ya jawo karuwar bukatar makamashi da ma'adinai, musamman kananan karafa daga kasashe masu tasowa.

A shekara ta 2010, bayan rikicin iyaka tsakanin China da Japan game da mallakar tsibirin Senkaku, kasar China, wadda ke kan gaba wajen samar da ma'adinan, sai ta ayyana takunkumi fitar da su zuwa kasar Japan, sannan ta karanta adadin da za a yi fitarwa zuwa wasu kasashe, musamman zuwa Yammacin Turai.

Wannan matakin ya kawo cikas ga manyan masana'antu, wanda hakan ya jawo hauhawar farashin ma'adanan a duniya.

A wannan lokacin ne Tarayyar Turai (EU) ta dawo da shirinta na nemo muhimman ma'adanan nan ta hanyar ayyana wasu ma’adinan da suke bukata a nahiyar.

A lokacin, babban kalubalensu shi ne samun hanyoyin samun wadannan ma’adinan ta hanyar sanya hanun jari a wuraren hako su, da zuba jari a kasashen, wadanda ba su da masaniyar arzikin da suke da shi.

A Yammacin Afirka baki daya, da yankin Sahel, da ke cikin yankuna da suka fi talauci a duniya, suna da wadatar arzikin da ke cikin kasa. Makashinsu da ma’adinansu ne ya sa kasashen “duniya da kungiyoyi suke sha’awarsu,” kamar yadda jaridar "l'Humanité" ta bayyana.

Mamayar ƙasa

Duba da yanayin dimbin arzikin ma’adinan da ke yankin, masana suna kiran yankin da, ‘yankin abin kunya.’

A yanzu, kamar yadda lamarin yake a baya, yawancin kamfanonin hako ma’adinai na kasashen Faransa ne, kamar su Orano da TotalEnergy, na Amurka irin su ConocoPhilips da ConocoPhilips da AngloAmerican da AngloGold Ashanti da BHP Billiton da Rio Tinto, CNCP na China. Sannan akwai kananan kamfanoni daga wadannan kasashen da suke fama da karyewar arziki.

Kamfanonin hako ma’adinan suna yaudarar kasashen Afrika ne, ta hanyar ba su hakkin mallakar wani dan karamin sashen albarkatunsu da ake kira one-penny, wato karamin hannun jari a kananan kamfanin hako ma’adinai da suke hada-hada a hannun jarin kasa da Dala 1 a Kasuwar Hannun Jarin Toronto da ke Amurka.

Akwai bukatar a fahimci cewa kasuwannin hannun jarin Toronto da Vancouver da Calgary na Canada ba su da adalci wajen sanya hannun jarin kamfanonin hako ma’adinan, wadanda yawanci suke shiga harkokin hako ma’adinan a yankin na Afrika.

Wadannan kamfanonin, wadanda ba su da hannun jarin ma’adinai da dama, wasu ma ba su da ofisoshi ko ma’aikata na dindindin, ba a sanin hakikanin mamallakansu, kuma suna bin bayan fage wajen tsallake biyan haraji, sannan sukan yi amfani da wasu dabaru wajen samun amincewar gwamnatocin kasashen Afrika wajen shiga yarjejeniyar hako ma’adinansu.

Da zarar an ba su kwantiragin, sai su garzaya wadancan kasuwannin hannun jarin saboda hannun jarinsu ya fara girmama, duk da cewa ba sa biyan haraji da hakkin muhalli da sauke hakkin mazauna yankunan da suke aiki, sannan kuma suke fara cin riba tun kafin ma a fara aikin.

Sannan ko sisi ba za su zuba jari ba, bayan watakila Dala miliyan 1 ko biyu da suke bayarwa a matsayin na goro domin samun kwangilar.

A bangaren kasuwancin ma’adinai, kasar Canada (Kasuwanncin hannun jarin kasar na Toronto da Vancouver) tamkar Zurich take ga masu almundahanar kudi da tserewa biyan haraji.

A shekara 30 da suka gabata, kasar Canada ta kasance kasar da ta fi maraba da masu harkokin hako ma’adinai.

Kamfanonin nan da dama suna ci da gumin kasashen Afrika ne. Ba mu manta yadda aka raba lasisin hako ma’adinai sama da 150 ba a yankunan Sahel na Liptako-Gourma da Sud Maradi da Air da Djado da yankin tafkin Tim Mersoi ga kamfanoni 42, (wasunsu ma na karya ne) daga kasashe 12 a shekarar 1995-96, wanda daga baya aka gane akwai cuwa-cuwa a ciki.

Me ya faru da wadannan lasisin guda 154 da Gwamnatin Nijar ta bayar a wancan lokacin, sannan me ya faru da kamfanonin da suka ci moriyar wannan tagomashin?

Yana kyau mu fahimci wani abu game da irin wadannan kamfanonin, wanda har yanzu ake jin duriyarsa: the Savannah Energy PLC, wanda a kwanakin baya aka tsince shi dumu-dumu da hannu wajen jawo lalacewar alakar diflomasiyya tsakanin kasar Kamaru da Chadi.

A wata sanarwar da Shugaban Kasar Chadi ya fitar a 23 ga Afrilun 2023, ya bayyana takaicinsa kan yadda aka samu sabani tsakanin kasashen biyu a kan sayan kadarorin ex-ESSO-Tchad da kamfanin Savannah Energy ya yi, inda Chadin ta zargi Kamaru da hannu wajen taimakawa ta rasa kadarorin wanda ke yankinta.

Guguwar sauyi

A cikin shekara goma da suka gabata, an samu karuwar kamfanonin Arewacin Amurka da Turai masu harkokin hako ma’adinai a Afrika.

Wannan sauyin da aka samu ya kara bayyana adawar da ke tsakanin kasashen Faransa da Amurka a yankin na Sahel, wanda a dabaibaye yake da wasu kirkirarrun matsaloli, wadanda ake amfani da su wajen assasa sansanonin soji da girke sojoji a yankin.

Lokaci ya yi da mutanen kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar za su fahimci abin da ya sa matsalar tsaron kasashensu ya ki ci, ya ki cinyewa, sannan su gane cewa rikice-rikice da kasancewar sansanonin sojin kasashen waje a yankinsu ba wani abu ne illa sha’awar ma’adinansu da makamashinsu da tun tuni ake kwashewa, (uranium a Nijar, da zinare a Mali da Burkina Faso), da kuma yunkurin kasashen waje wajen ganin sun zuba hannun jari a sababbin ma’adinan da ba a fara hakowa ba, (kamar yarjejeniyar hako ma’adinin leonine da aka yi a wasu kasashen a kwanan nan.)

Yanayin ci-gaban wasu fasahohin a zamanin mulkin mallaka da bayansa ne suka jawo tafiyar hawainiya wajen hako ma’adinan nan, amma yanzu duniya na matukar bukatarsu, sannan kasashen Yamma ba za su taba hutawa ba har sai sun same su.

Da alama yanayin wayewa da fafutikar matasan na kawo cikas ga tsare-tsaren kasashen Yammacin Turai.

Yanzu alamu sun fara nuna cewa yadda kasashen Yammacin Turai suke wawushe albarkatun kasashen yankin Sahel ya fara samun cikas, kuma da alama wannan gumurzun ma yanzu aka fara.

An fara wallafa wannan ra’ayin na a shafin TRT World a Agustan 2023. Marubucin, Mahaman Laouan Gaya, tsohon Minista ne a Jamhuriyar Nijar, sannan tsohon Sakatare Janar na Kungiyar Kasashe Masu Albarkatun Man Fetur, (APPO).

Togaciya: Ba dole ra’ayin marubucin ya zama ya yi daidai ra’ayi ko ka’idojin aikin jarida na TRT Afrika.

TRT Afrika