Kulob ɗin Bodo/Glimt ta tattara duka kuɗaɗen da aka tara daga sayar da tikitin wasan da ta buga da ƙungiyar Maccabi Tel Aviv ta Isra'ila a Gasar Europa ta aika Gaza.
Ƙungiyar da ke ƙasar Norway tana alfahari da sadaukarwarsu wajen “samar da ƙaƙƙarfan tallafi a yanayin rikici da duniya ke ciki”.
Sakamakon wannan ne, ƙungiyar ta ayyana bayar da kuɗin da ya kai fam miliyan 52,000 don ayyukan jinƙai a yankin Gaza.
Wannan cigaba na zuwa ne yayin da lamura suka ta'azzara a rikicin Isra'ila da Hamas, Bodo/Glimt ta samu ƙalubale da dama wajen ɗaukar baƙuncin wasan da suka buga da Maccabi Tel Aviv a filin wasa na Aspmyra.
Sai dai wasan ya gudana, amma an kalle shi a matsayin “alama ta haɗin-kai, zaman lafiya, da juriya”.
Frode Thomassen, shugaban kulob ɗin Bodo/Glimt, ya ce game da yunƙurin haɗa kan al'ummomi da magance matsalolin da suka wuce iyakokin filin ƙwallo: “Mu a FK Bodo/Glimt ba za mu kau da kai daga wahalar ake gani da saɓa dokokin duniya a wasu ɓangarorin duniya ba.
“Duk da kulob ɗin ƙwallo ne, ba na siyasa ba, mun lura da nauyin cewa sai mun ba da tallafi don kawo kyakkyawan sauyi.
"Shi ya sa muka zaɓi ba da kyautar kuɗin shigar da muka samu daga wannan wasa ga Red Cross, don a yi aikin agaji a yankin Gaza.”
Inge Henning Andersen, shugaban kulo din Bodo/Glimt ya ƙara da cewa: “Wannan gudunmawar ta fi gaban a cewa ɗan tallafi kawai; saƙo ne na tausayi da goyon baya.
"Ta wannan aikin, muna da burin nuna cewa ƙungiyarmu tana tare da waɗanda ke cikin yanayi na buƙata, kuma wasa na iya zama wani abu da zai yi kyakkyawan tasiiri fiye da buga tamaula a filin ƙwallo.