Altun ya bayyana cewa taba addini da suke yi a bayyane take suna neman tayar da rikici ne. Photo/AA

Daraktan watsa labarai na Turkiyya Fahrettin Altun ya yi tir da kuma Allah wadai da ci gaba da “wulakanta” Alkur'ani Mai Girma da kuma tutar kasar Turkiyya da ake yi a Denmark.

“Bai kamata hukumomin Denmark su rinka daukar wannan lamari na nuna kiyayya ga Musulunci da nuna kiyayya ga baki da wariya ba a matsayin hakkin bayyana ra’ayi. Ba za a amince da wannan ba kuma hakan hatsari ne,” kamar yadda Altun ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Martanin nasa na zuwa ne bayan mambobin kungiyar masu tsatsauran ra’ayi ta Patrioterne Gar Live sun taru a wajen ofishin jakadancin Turkiyya da ke Copenhagen inda suka kona Alkur'ani da kuma tutar kasar Turkiyya.

Altun ya bayyana cewa amfani da abubuwa masu tsarki da kuma wasu alamomi da niyyar tayar da rikici ba za a kira shi ‘yancin tofa albarkacin baki ba, inda ya kara da cewa Turkiyya tana martaba addinai da sauran al’ummomi a fadin duniya, kuma tana bukatar su ma Turawa su yi hakan.

“Akwai bukatar gwamnatocin kasashen Turai da kuma kungiyoyi masu zaman kansu su dauki mataki yanzu, ba sai anjima ba, domin dakile wadannan ayyuka na ta’addanci da karfi da yaji muddun suna so a yi tattaunawa cikin zaman lafiya tsakanin addinai daban-daban da al’adu. Kada su bari wadannan masu tunzuran su baza kiyayyarsu,” kamar yadda Altun ya kara da cewa.

Haka kuma ya yi kira ga hukumomin Denmark da su dauki matakai kan wadannan masu tunzurin da kuma daukar wasu matakan na kiyaye afkuwar irin wadannan lamura a gaba.

Tun da farko dai, ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta bayyana cewa kasar ba za ta taba amincewa da “mugayen abubuwan da ake bari ana yi ba da sunan ‘yancin bayyana ra’ayi.”

Ma’aikatar ta gayyaci jakadan Denmark a Ankara Danny Annan domin jan hankalin hukumomin Denmark don su dauki mataki kan wadanda suke da hannu a wannan lamari.

TRT World