Zaɓukan da aka yi na magadan birane sun nuna ƙarfin dimokuraɗiyyar Turkiyya./Hoto: TRT World

A yayin da ake yi wa 2024 take a matsayin shekarar zaɓuka a duniya, Turkiyya ta kammala zaɓukan magadan birane a larduna 81 – waɗanda sakamakonsu ya nuna jajircewarta wajen gudanar da sahihan zaɓuka, a cewar masu sharhi.

Da alama babbar jam'iyyar hamayya CHP ta samu nasarori, inda take kan gaba a zaɓukan magadan birane 15 cikin 30, waɗanda suka haɗa da Istanbul, Ankara da Izmir, abin da masana suke gani a matsayin wani abu da ya fito da ra'ayin ƴan ƙasa ko da yake bai sauya tsarin shugabancin ƙasar ba.

A cewar wani masanin siyasa da ke Istanbul Onur Erim, zaɓuka wasu lokuta ne na biki ga Turkawa domin kuwa an yi su cikin tsaro sosai idan aka kwatanta da shekarun baya lokacin da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya hau kan mulki.

“Yanzu ba a matsa wa mutane lamba kan jam'iyyar da ya kamata su zaɓa. Akwai lokacin da ƴan ta'adda na PKK [a wasu larduna] suke faɗar sakamakon zaɓuka a shekaru 15 zuwa 20 da suka wuce. Yanzu hakan ba ya faruwa,” in ji Erim a hira da TRT World.

Sakamakon wucin-gadi ya nuna cewa Jam'iyyar CHP tana kan gaba a manyan birane duk da yake Jam'iyyar AK Party tana kan gaba a gundumomi 366 yayin da CHP take biye da ita da gundumomi 333 a lokacin rubuta wannan labari, lamarin da ya ƙaryata labaran kafafen Yammacin Turai cewa zaɓukan Turkiyya ba su da sahihanci a zamanin mulkin Erdogan.

“Wannan zaɓen ya fallasa masana da dama da ke sukar Turkiyya cewa ita ƙasa ce mai kama-karya. Babban saƙon da aka tura wa kasashen duniya shi ne Turkiyya ƙasa ce mai ƙarfin dimokuraɗiyya. Fitowar da kashi 70 cikin ɗari na ƴan ƙasar suka yi don kaɗa ƙuri'a babban lamari ne. A ƙasashen Turai, mutanen da ke fitowa don jefa ƙuri'a a ƙananan zaɓukan ba su wuce kashi 30 ba,” a cewar Tarek Cherkaoui, wani mai nazari kuma manaja a Cibiyar Bincike ta TRT World Research Centre.

TRT World