Isra'ila na ci gaba da kashe mutane a Gaza a kullum waɗanda akasarinsu yara ne da mata. / Hoto: Reuters

1415 GMT — Sojojin Isra'ila sun ce an yi musayar wuta da dakarun Masar

Sojojin Isra'ila sun sanar da cewa an yi musayar wuta da dakarun Masar a ranar Litinin a kan iyakar Rafah da ke tsakanin Masar da zirin Gaza.

“A ‘yan sa’o’i da suka gabata, an yi harbi a kan iyakar kasar Masar, ana gudanar da bincike kan lamarin. Ana tattaunawa da bangaren Masar,” in ji sanarwar da rundunar ta fitar.

Kafar yada labaran Isra'ila ta KAN ta ce an kashe wani sojan Masar a harin da aka kai.

1057 GMT — Hezbollah ta sanar da kai hari ga sojojin Isra'ila

Hezbollah a ranar Litinin ta bayyana cewa ta kai hari kan wani gini da sojojin Isra'ila ke amfani da shi a arewacin Isra'ila.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce ta kai hari kan wani gini da sojojin Isra'ila ke amfani da shi a matsugunin Margaliot da "makaman da suka dace," inda suka ce sun samu "tabbataccen sakamako."

Tashar talabijin ta Channel 12 ta Isra'ila ta bayar da rahoton faruwar lamarin a safiyar yau litinin, inda ta ce wani makami mai linzami da aka harba daga kasar Lebanon ya fada wani gini a garin Margaliot.

1025 GMT — Akwai yiwuwar harin Rafah ya kawo 'cikas' kan yarjejeniyar tsagaita wuta

Akwai yiwuwar munanan hare-haren da Isra'ila ta kai birnin Rafah da ke kudancin Gaza ya kawo cikas ga yarjejeniyar tsagaita wutar da ake yunƙurin yi ta musayar fursunoni, kamar yadda ƙasar Qatar wadda ke shiga tsakani ta bayyana.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana "damuwa da cewa tashin bam din zai dagula kokarin shiga tsakani da ake yi da kuma kawo cikas ga cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta nan take."

Kasar Qatar, tare da Amurka da Masar, sun shafe watanni suna tattaunawa da nufin ganin an cimma matsaya tsakanin Isra'ila da Hamas a yankin Gaza da Isra'ila ta wargaza.

TRT Afrika da abokan hulda