'Yan Falasdinu da kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun jima suna kokawa kan yadda Isra'ila ta ki dakatar da ayyukan tashin hankali kan mazauna yankunanta. / Hoto: AA

Turkiyya ta yi Allah-wadai kan yaga littafin Alkur’ani mai tsarki na addinin Musulunci da mazauna Isra'ila wadanda suka ruguza wani masallaci a garin Urif da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan suka yi.

"Muna yin Allah-wadai da harin da wasu gungun Yahudawa 'wadanda suka yaga littafinmu mai tsarki na Alkur'ani, bayan shiga wani masallaci a garin Urif da ke yankin Falasdinu wanda ke karkashin mamayar Isra'ila," a cewar sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar ta fitar a ranar Alhamis.

“Muna bukatar a gurfanar da wadanda suka aikata wannan mummunan laifi na nuna kiyayya da gaggawa a gaban kuliya,” a cewar sanarwar.

Turkiyya ta bayyana damuwarta game da sabon tashin hankalin da ya barke a 'yan kwanakin nan a yankin.

Kazalika ma'aikatar ta yi tir tare da Allah-wadai da kakkausar murya kan yawan hare-haren da kungiyoyin mazauna yankin wadanda ke zama ba bisa ka'ida ba ke kai wa sassa daban-daban na Yammacin Kogin Jordan da kisan gillar da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka yi wa wani Bafalasdine.

Har ila yau, sanarwar ta yi nuni da cewa, Isra'ila na da hakki karkashin dokokin kasa da kasa na hana duk wani hari kan al'ummar Falasdinawa da wuraren ibadarsu da wuraren zamansu da dukiyoyinsu da kuma hana aikata laifukan nuna kiyayya, ciki har da wadanda ke da nasaba da nuna kiyayya ga addinin Musulunci.

Babban tashin hankali

A 'yan watannin baya-bayan nan dai ana zaman dar-dar a yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye sakamakon yawan hare-hare da Isra'ila ke kai wa garuruwan Falasdinawa.

Kusan Falasdinawa 180 ne sojojin Isra'ila suka kashe tun daga farkon wannan shekarar, a cewar ma'aikatar lafiya.

A kalla ‘yan Isra’ila 25 ne kuma aka kashe a hare-hare daban-daban a tsakanin lokacin.

Kasashen duniya na adawa da kafa matsugunan a yankunan Falasdinu da aka mamaye ba bisa ka'ida ba.

Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, da shugabannin gwamnatinsa suka yi kaurin suna wajen nuna iko kan batun mazuna yankin da ke zaune ba bisa ka'ida masu musu biyayya.

Isra'ila ta karbe ikon yammacin Gabar Kogin Jordan da Gabashin Kudus da Gaza a yakin tsakaninta da Larabawa a shekarar 1967.

A 2005 ta janye sojojinta daga Gaza, kuma tun daga lokacin ta sanya wani katafaren shinge na kasa da sama da kuma ta kan ruwan da ya raba ta da Falasdinu, lamarin da ya hana daukacin al'ummar kasar fita ko shiga Gaza tare da takaita shiga da ficen kayayyaki kasar.

Fiye da 'yan Isra'ila 700,000 ne da ke zama ba bisa ka'ida a Yammacin Gabar Kogin Jordan tare mamaye Gabashin Kudus.

TRT World