Wasu da ake zargin ‘yan nazi ne sun kaiwa matsugunan ‘yan gudun hijira a Jamus

Kafafan yada labarai sun rawaito cewan an kona matsugunin ‘yan gudun hijirar Yukren a arewacin Jamus.

Babu wani daga cikin ‘yan gudun hijirar su 14 da ya samu rauni a yammacin Laraba, a yayin da hayaki ya turnuke a ginin, wanda a baya ake amfani da shia matsayin otel a yankin Gross Stromkendorf, garin dake jihar Mecklenburg-Western Pomerania.

Helkwatar ‘yan sandan Rostock ta fitar da sanarwar cewa suna zargin sunza zargin akwai siyasa a lamarin, kuma an kafa kwamitin bincike karkashin mukadasshin shugaban sashen bayar da kariya na jihar.

An ga rubutun Swastika

‘Yan sanda sun ziyarci matsugunin a karshen mako bayan da aka ga an fesa Swastika a jikin kofar shiga, kamar yadda kafafan yada labaran yankin suka rawaito.

Jami’İn gundumar Tino Schomann ya shaidawa manema labarai cewa “Daga shekarun da na samu kwarewa na aiki a matsayin mai kashe gobara, na fahimci da gangan aka cinna wannan wutar.”

Sashen kwana-kwanan kuma ya bayyana cewa, dole aiyukan gaggawa suka kyale ginin ya cinye saboda yadda ba za a iya shawo kan wutar ba.

An mayar da ‘yan gudun hijirar zuwa wani gin,n da gwamnati ta samar musu.

Gobarar da aka samu a yankin jihar Mecklenburg-Vorpommern matalauciya dake gabas, ta afku ne a kusa a wajen da a watan Agustan 1992 daruruwan masu tsaurin ra’ayi suka yi zanga-zangar nuna adawa ga masu neman mafaka a Jamus har tsawon kwanaki biyu, inda suk dinga jefa bama-bamai kan matsugunan ‘yan gudun hijira, wanda wannan ne nuna adawa ga ‘yan gudun hijira a Jamus mafi muni tun bayan yakin Jamus.

Rikicin ya mamaye dukkan kasar Jamus, inda mabiya Nazi suka dinga kona gidajen Turkawa a Solingen.

TRT Afrika da abokan hulda