SIYASA
3 minti karatu
Kotu a Bangladesh ta tura manyan hafsoshin soji gidan yari a wata shari’a ta tarihi
Manyan hafoshin, ciki har da janar-janar biyar, an zarge su da laifin kafa wani ɓoyayyen wurin tsare mutane a lokacin mulkin Firaminista, Sheikh Hasina, wadda aka kora a mulki.
Kotu a Bangladesh ta tura manyan hafsoshin soji gidan yari a wata shari’a ta tarihi
Dakarun tsaro suna girke a gaban babban gidan gyara hali na Dhaka . / AA
9 awanni baya

Wata kotu a Bangladesh ta tasa ƙeyar manyan hafsoshin soji 15  — ciki har da hafsoshi 14 da ke bakin aiki— zuwa gidan gyara hali kan tuhume-tuhume na tilasta ɓacewar mutane da kuma zalunci da aka aikata a lokacin tawayen da ɗalibai suka jagoranta wanda ya hamɓarar da gwamnati a shekarar 2024.

Ranar Laraba, kotun hukunta laifukan yaƙi da ke Dhaka ta kuma ba da umarnin wallafa sammaci a shafukan jaridu ga tsohuwar shugabar ƙasar Sheikh Hasina, wadda ta tsere da mai ba ta shawara kan tsaro da sauran mutane da ke da hannu a lamarin.

Wannan shi ne karo na farko da aka gabatar da tuhuma kan tilasta ɓacewar mutane a Bangladesh, kuma shi ne karon farko da manyan hafsoshin soji masu yawa suka fuskanci shari’a.

Mutanen, ciki har da janar-janar biyar, ana zarginsu ne da jagorantar wata ɓoyayyiyar cibiyar tsare mutane a lokacin mulkin Firaminsta Sheikh Hasina wadda aka hamɓarar.

Dukkansu sun yi aiki a ɓangaren tattara bayanan sirrin sojin ko kuma rundunar RAB wadda ke tsoratar da mutane.

Rundunar sojin ƙasar ta ce za ta taimaka wajen shari’ar, amma akwai yanayin zaman ɗarɗar tun lokacin da kotun ta ba da sammacin kama su da farkon wannan watan.

"Sun bayyana mubaya’arsu ga dokar ƙasar da kuma biyayyarsu ga matakan shari’ar," kamar yadda babban mai gabatar da ƙara Tajul Islam ya bayyana wa manema labarai.

"An bayyana wannan a cikin hadin kan da suka bayar."


‘Wani lokaci mai muhiummanci’

Babban jami’in ‘yancin bil Adama na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD), Volker Turk, a wata sanarwar da ya fitar ranar 15 ga watan Oktoba, ya ce shari’ar kotun wani muhimmin mataki ne na tsaga gaskiya.

"Wani lokaci mai muhimmanci ne ga waɗanda lamarin ya rutsa da su da iyalansu," a cewar Turk.

A motar gidan yari ne aka kawo hafsoshin kotun, wadda ‘yansanda da yawa ke karewa.

Bangladesh ta gurfanar da manyan jami’an gwamnatin da ta shuɗe da ke kusa da Hasina — wadda a halin yanzu tana gudun hijira a India — da kuma jam’iyyarta ta Awami League wadda a halin yanzu an soke ta.

An kashe mutum 1,400 a arangama tsakanin watan Juli da watan Agusta na shekarar 2024 yayin da dakarun tsaron suka yi ƙoƙarin murƙushe zanga-zangar ƙin gwamnati, in ji MDD.

A lokacin mulkin Hasina, rundunar RAB ta aiwatar da wasu kashe-kashe, kuma Amurka ta ƙaƙaba wa rundunar takunkumi a shekarar 2021.

Hasina, mai shekara 78, ta stere a shekarar da ta gabata zuwa birnin New Delhi, inda ta saɓa wa umarnin kotu na halatartar shari’arta da ake yi kan laifukan cin zarafin bil’adama domin umarnin murƙushe zanganzagar da ta bayar.

Shari’ar da ake yi a bayanta (Hasina) tana ƙarshe-ƙarshe, inda masu kare Hasina waɗanda gwamnatin ƙasar ta samar ke gabatar da jawabinsu na ƙarshe. Masu gabatar da ƙara sun nemi a yanke wa Hasina hukuncin kisa.

Jam’iyyar Awami Leagua ta Hasina ta ce ta musanta tuhume-tuhumen “ƙarara.”