Lailatul Qadri: Dare guda mai darajar watanni 1,000
A lokacin Ramadan, Musulmai suna ƙara yawan ibada. / Others
Lailatul Qadri: Dare guda mai darajar watanni 1,000
A kwanaki goma na ƙarshen Ramadan ake sa ran ganin daren Lailatul Qadri.
14 awanni baya

A addinin Musulunci, dare guda yakan fi darajar fiye da watanni dubu. Ana kiran wannan dare da Lailatul Qadr, ma'ana Daren Ƙudra ko Daren Ƙaddara.

Ana samun sa a watan Ramadana wata mai tsarki na Musulunci, inda Musulmai a faɗin duniya ke ƙara ibada don ƙarfafa imani, ciki har da azumi, da sallolin dare na musamman, da addu’i’o, da karatun Alkur'ani.

A bisa koyarwar Musulunci, Dare Lailatul Qadr na faruwa ne a cikin ranakun goma na ƙarshen Ramadana.

Ko da yake ba a san daidai ranar ba, malaman addini sun bayyana cewa yiwuwar ganinsa ta fi yawa a ranakun 21, 23, 25, 27, da 29 na watan.

“Wannan shi ne dare mafi muhimmanci ga Musulmai,” in ji Imam Shariff Hassan, wani malamin addini, a cikin hudubar Ramadana da ya yi a Mombasa, Kenya.

Mala'iku na sauka zuwa duniya

Wasu Musulman na zama tsawon duka kwanaki goman a masallaci, suna ibadar da ake kira Itikaf, don sadaukar da kansu da lokutansu wajen bautar Allah.

Masana addina suna kuma cewa daren yakan kasance mafi nutsuwa da salama, inda sararin samaniya yakan bayyana garai sama da al'ada, kuma akan samu iska mara ƙarfi.

Sauran alamun sun haɗa da cewa rana na iya fitowa da safe da haske mara tsanani, ba tare da kyalkyali mai ƙarfi ba.

A Daren Lailatul Qadri ne ne Annabi Muhammadu (tsira da aminci su tabbata a gare shi) ya sami wahayi na ayoyi na farko na Al-Qur'ani, ta hannun Mala'ika Jibrilu.

A zahiri ma, akwai cikakkiyar sura a cikin AlKur'ani mai sunan wannan daren, wato Surah Al-Qadr — wadda a cikinta Allah ya ce, “Daren Ƙaddara ya fi watanni dubu.”

Ana iya gafarta dukkan zunubai

“Sakamakon ibada a wannan dare kaɗai ya fi daraja fiye da dukkan ibada a cikin rayuwa,” in ji Imam Shariff.

Malaman addini suna bayanin cewa, a wannan dare dubban mala'iku na sauka duniya suna yin addu'o'i ga waɗanda ke roƙo da waɗanda ke tsayuwar dare. Amma ba kowa ba ne ke sa'ar shaida daren ko ya ga alamunsa.

A koyarwar Musulunci, idan ka shaida daren kana cikin ibada da neman tuba da gaske, Allah zai gafarta maka duka zunubanka. A cewar AlKur'ani, a wannan ne dare ake ƙaddara makomar mutane na shekara-shekara.

Ga kusan Musulmai biliyan biyu a duniya, wannan shi ne dare mafi girma a cikin shekara.

Imam Shariff ya kammala da cewa, “Ga 'yan uwa maza da mata, muna tunatar da su cewa wannan dare na ba da wata dama mai wuyar samu. Wato wata dama ce ta sake lale, da neman gafara, da sabunta imani”.