| Hausa
RAYUWA
2 minti karatu
An haifi wasu ‘yanbiyun gwaggwon biri da ke da wuyar samu karo na biyu a Congo DRC
Masana na kallon haihuwar ‘yanbiyu a tsakanin gwaggwon biri na tsauni, musamman nau'in "mountain gorilla” a Turance da ke fuskantar barazanar ƙarewa, a matsayin wani abu da ba a saba gani ba.
An haifi wasu ‘yanbiyun gwaggwon biri da ke da wuyar samu karo na biyu a Congo DRC
Sabuwar haihuwar gwaggwon birin 'yanbiyu ta biyo bayan haihuwar wasu tagwaye a Virunga National Park a watan Janairun 2026. Hoto / Virunga Park / Others
17 awanni baya

A wani lamari mai ban mamaki da ya faru a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, an haifi wasu ‘yanbiyun gwaggwon biri kwanan nan a Gandun Dajin Virunga, wani waje da ya yi fice da albarkatun halittu amma yake fuskantar barazanar rikice-rikice.
 
"Wadannan ‘yanbiyu, wadanda aka yi amannar mace da namiji ne, suna da kimanin mako biyu da haihuwa, kuma jami'ai na sanya ido sosai a kan su," in ji hukumar kula da gandun dajin a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata.
 
An bayar da rahoton makamancin wannan lamari a watan Janairu a wannan gandun daji, inda aka samu haihuwar ‘yanbiyu maza.
 
Duk da wadannan abubuwan da suka faru kwanan nan, masana na daukar haihuwar ‘yanbiyu a tsakanin gwaggwon biri a matsayin wani abu da ba kasafai ake gani ba.
 
"Samun ‘yanbiyu a tsakanin gwaggwon biri wani lokaci ne na musamman duba da ƙarancin faruwar hakan," in ji Tara Stoinski, Shugabar Gudanarwa kuma Babbar Jami'ar Kkimiyya ta Gidauniyar Dian Fossey Gorilla Fund, yayin tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na AFP.
 
"Bincikenmu na kusan shekaru 60 a kan bayanan gwaggwon biri ko tsauni... ya nuna mana cewa hakan yana faruwa ne a kasa da kashi daya cikin 100 (1%) na duk haihuwar da ake yi."
 
Rayuwar yantagwayen babban kalubale ne domin "ba wai kawai uwar sai ta goyi jarirai biyu ba ne, wanda hakan ke sa tafiya ta yi mata wahala musamman a makonnin farko... dole ne kuma ta samar da karin madara, wanda hakan ke bukatar kuzari mai yawa daga jikinta," in ji Stoinski.
 
Gandun Dajin Virunga shi ne wurin kula da namun daji mafi dadewa a Afirka, wanda aka kaddamar a shekarar 1925, kuma yana cikin jerin wuraren tarihi na musamman a duniya na UNESCO.
 
Amma karuwar rikice-rikice a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, inda kungiyar mayakan M23 ta kwace yankuna da dama a shekarun baya-bayan nan, yana barazana ga wannan waje.
 
Haka kuma, ana kyautata zaton wasu mayakan kungiyar ta'addanci ta ADF na amfani da dazuzzukan Virunga a matsayin maboya.
 
A duk duniya, an kiyasta cewa akwai gwaggwon biri na dutse guda 1,063 ne kacal da ke rayuwa a daji, inda aka kiyasta akwai kusan guda 350 a cikin gandun dajin Virunga a shekarar 2021, a cewar hukumomin gandun dajin.