NIJERIYA
2 minti karatu
Dakarun Nijeriya sun kuɓutar da mutanen da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su Jihar Kogi
Sanarwa ta ce da dakarun sun samu bayanai game da aika-aikar ɓarayin dajin, sai suka nufi inda suke a dajin Achigili da ke Jihar Kogi.
Dakarun Nijeriya sun kuɓutar da mutanen da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su Jihar Kogi
Nijeriya tana fama da matsalolin tsaro ciki har da garkuwa da mutane / AP
11 awanni baya

Sojin Nijeriya sun yi sanar da kuɓutar da mutum biyu da aka yi garkuwa da su a Jihar Kogi da ke arewa maso tsakiyar ƙasar.

A wata sanarwa da muƙaddashin mataimakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ta 12 ta sojin Nijeriya, Laftanar Hassan Abdullahi, ya fitar ranar Lahadi, rundunar sojin ta ce dakarun sun ƙwato kuɗin fansa daga masu garkuwa da mutanen.

“Aikin da ya yi silar ‘yanta waɗanda lamarin ya rutsa da su an yi shi ne ranar 2 ga watan Nuwamba na shekarar 2025, bayan an samu bayanan sirri kan ayyukan masu garkuwa da mutane a yankin Itobe–Adumu–Ejule,” in ji sanarwar.

Sanarwa ta ce yayin da dakarun suka samu bayanai game da aika-aikar ɓarayin dajin, sai suka nufi inda suke a dajin Achigili da ke jihar.

Sai dai kuma kafin su isa wurin sai masu garkuwa da mutanen suka buɗe musu wuta, in ji sanarwar.

Nan-take dakarun suka mayar da martani inda ƙarfin makaman sojojin ya fi na ɓarayin, lamarin da ya sa suka tsere kuma suka bar waɗanda suka yi garkuwa da su ɗin da kuɗin fansar da suka tara.

“Bayan arangamar, dakarun sun ‘yanta waɗanda lamarin ya rutsa da su tare da kuɗi ₦3,800,000 (naira miliyan uku da dubu ɗari takwas) wanda suke ƙoƙarin amfani da shi a matsayin kuɗin fansa. Kuma nan-take aka yi wa waɗanda aka kuɓutar tambayoyi, “ in ji sanarwar.