Rasha tana sa ido sosai kan rahotannin da ke cewa Amurka na iya la'akari da daukar matakin soja a Nijeriya, in ji mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha, Maria Zakharova, tana mai kira ga Washington da ta yi aiki bisa ka’idojin dokokin kasa da kasa.
“Muna bibiyar wannan batu sosai kuma muna kira ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa su bi ƙa’idojin dokokin ƙasa da ƙasa a tsanaki,” in ji Zakharova a ranar Jumma’a yayin wani taron manema labarai na mako-mako a Moscow, tana mayar da martani kan tambaya game da halin da ake ciki a kasar ta Afirka.
Maganganunta sun biyo bayan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump a ranar 1 ga Nuwamba, inda ya ce ya umarci Ma’aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) da ta tsara yiwuwar ɗaukar matakin soja domin “kare al’ummomin Kirista” a Nijeriya.
Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance daga Washington kan irin wannan shiri, kalaman Trump sun ja hankalin ƙasashen waje, inda Moscow ta jaddada mahimmancin mutunta ikon mallakar ƙasa da bin dokokin ƙasa da ƙasa.
Tuni Nijeriya ta musanta ikirarin Amurka kan cin zarafin Kiristoci a kasar.
A wannan makon Ministan Harkokin Wajen Nijeriya ya yi gargaɗi game da yunƙurin da ake yi domin taɓarɓarar da al’amura.
“Abin da muke kokarin fahimtar da duniya shi ne kada mu ƙirƙiri wata Sudan ta daban,” in ji Ministan Harkokin Wajen Nijeriya Yusuf Tuggar a ranar Talata.
“Mun ga abin da ya faru da Sudan, tare da matsin lamba na raba Sudan bisa addini, bisa tunanin kabilanci,” in ji shi.












