| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
'Yanwasan Senegal sun samu kyautar kuɗi da fuloti saboda lashe Kofin AFCON
Shugaba Bassirou Diomaye Faye ya ba da kyautar makudan kuɗi da ya kai $134,892.09 ga kowanne daga cikin 'yanwasan 28, da kuma filaye.
'Yanwasan Senegal sun samu kyautar kuɗi da fuloti saboda lashe Kofin AFCON
Sadio Mané na Senegal ya ɗaga Kofin Nahiyar Afirka. / Reuters
22 Janairu 2026

Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye ya bai wa kowane ɗanwasa na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar kyautar fiye da dala 130,000, tare da fili a bakin teku, bayan nasarar da suka samu a wasan ƙarshe na Gasar Kofin Afirka a ranar Lahadi a Maroko.

Shugaban ya yi magana a wani biki a babban birnin Dakar a daren Talata, inda dubban magoya baya suka fita titi don tarbar tawagar ta “Zakunan Teranga” waɗanda suka koma gida da kofi.

Senegal ta doke mai masaukin baƙi, Maroko da ci 1-0, a wani wasa da 'yanwasan Senegal suka bar filin wasa na wani ɗan lokaci, sakamakon ba da bugun ɗurme ga Maroko ana dab cika minti 90 na wasa.

Bayan 'yanwasan Senegal sun koma filin, Maroko ta zubar da fanaretin, sannan Pape Gueye ya ciyo ƙwallo guda, cikin mintuna huɗu bayan fara zangon ƙarin lokaci.

A daren Talata, 'yanwasan Senegal sun hau saman bas da aka rubuta “Zakunan Afirka” yayin wani zagaye da suka yi a Dakar zuwa Fadar Shugaban Ƙasa.

Girmama Senegal

An yi wa kowanne daga cikin 'yanwasan 28 kyautar CFA miliyan 75 (kimanin dala $134,892.09), wanda jimillarsu ta kai CFA biliyan 2.1 ko kusan dala miliyan 3.7. Haka nan za a ba su fuloti mai faɗin murabba'in mita 1,500.

Bugu da ƙari, Shugaba Faye ya ce jami’an ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Senegal za su sami CFA miliyan 50 da fuloti mai faɗin murabba'in mita 1,000, yayin da mambobin tawagar Senegal da suka je Maroko za su sami CFA miliyan 20 da fuloti mai faɗin murabba'in mita 500.

Ya ce ma'aikatan ma'aikatar wasanni za su samu ladan jimilla CFA miliyan 305.

Shugaba Faye ya ce a ranar Talata yayin da yake jawabi ga ‘yan tawagar Fadar Shugaban Ƙasa: “Ya ku Zakuna, kun girmama tutar da aka ɗora muku. Kun girmama Senegal. Kun nuna misalin cewa idan mutanen Senegal suka ci gaba tare da ladabi da tabbaci, babu wani ƙalubale da ya wuce ƙarfinsu.”

Senegal ta lashe Gasar Kofin Afirka karo na farko a 2021, lokacin da ta doke Masar a wasan ƙarshe. A lokacin, an ba 'yanwasa ladan CFA miliyan 50 da fulotai mai faɗin murabba'in mita 200.