| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
4 minti karatu
Ali Larijani: ‘Gwarzon Wannan Lokaci’ wanda ya haɗa tsoffin jini da sabbin jinin Iran
Masu sharhi da dama suna bayyana Larijani a matsayin “gwarzon wannan lokaci.”
Ali Larijani: ‘Gwarzon Wannan Lokaci’ wanda ya haɗa tsoffin jini da sabbin jinin Iran
Ali Larijani: Mutumin da ya daɗe yana mai faɗa aji kuma ya jagoranci majalisar dokoki a muhimman lokuta. / Reuters
3 awanni baya

Gogaggen ɗan siyasar ya riƙe manyan mukamai a bangaren tsaro, yaɗa labarai, da majalisar dokokin Iran na tsawon shekaru 40.

An kashe Ali Larijani, Sakataren Majalisar Koli ta Tsaro ta Iran, a wani harin sama da Isra’ila ta kai a Tehran. Wannan ya kawo ƙarshen ayyukansa na shekaru 40, inda ya tashi daga matsayin kwamandan dakarun juyin juya hali (IRGC) zuwa babban jigo a dabarun tafiyar da Jamhuriyar Musulunci.

Masu sharhi da dama suna bayyana Larijani a matsayin “gwarzon wannan lokaci.”

Ana kallon salon takunsa a matsayin mai matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da haɗin kan tsarin gwamnatin Iran a lokacin rikice-rikicen mika mulki bayan kisan tsohon Jagoran Addinin Kasar Ali Khamenei a ranar 28 ga Fabrairu, har zuwa naɗin sabon jagora, Mojtaba Khamenei.

Shekarunsa a harkokin siyasa da shugabanci

An haifi Larijani ranar 3 ga Yuni, 1957 a birnin Najaf na ƙasar Iraki. Ya fito ne daga ɗaya daga cikin manyan gidajen siyasa na Iran.

Tarihin karatunsa yana da zurfi kamar yadda harkokin siyasasa suka kasance masu zurfi; ya kammala digirinsa na farko a fannin kimiyyar kwamfuta (Computer Science) a jami’ar fasaha ta Sharif, kafin ya samu digirin digirgir a fannin falsafa (Philosophy) daga jami’ar Tehran.

Wannan zurfin ilimin da ya samu ya taimaka masa wajen yin amfani da dabarun nazari da lissafi a cikin ayyukansa na diflomasiyya da na majalisa daga bisani.

Ya fara aikinsa ne a shekarar 1981 a matsayin shugaban sashen labarai na ƙasa, amma jim kaɗan ya koma ɓangaren soja, inda ya fara aiki da dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) a shekarar 1982.

A karshen shekarun 1980, ya yi aiki a manyan muƙaman shari’a da na majalisa a cikin ma’aikatar dakarun juyin juya hali, har ya zama mataimakin babban hafsan dakarun IRGC tsakanin 1994 zuwa 2004.

Daga kafofin watsa labarai zuwa fannin nukiliya

A shekarun 1990, Larijani ya mayar da hankali kan al’adu da dabarun yada manufofin kasa.

A matsayinsa na shugaban kamfanin yaɗa labarai na gwamnati (IRIB) na tsawon shekaru goma (1994–2004), ya taka rawa sosai wajen sarrafa yadda ake bayar da labarai a cikin gida.

Sai dai, komawarsa Majalisar Koli ta Tsaro ta Ƙasa ce ta sa aka san shi a fagen duniya.

A matsayinsa na jami’in da ke kula da batun nukiliyar Iran a lokacin shugabancin Mahmoud Ahmadinejad, Larijani ya kasance jigo a tattaunawar ƙasa da ƙasa mai cike da sarkakiya.

Likafarsa ta kara yin gaba lokacin da ya koma majalisar dokoki. An zaɓe shi a matsayin wakili birnin Qom, kuma ya yi aiki a matsayin Shugaban Majalisar Dokoki har sau uku a jere daga 2008 zuwa 2020.

Duk da cewa ana kallonsa a matsayin mai ra’ayin rikau, an san shi da ikon yin sulhu da masu ra’ayin matsakaici, inda ya taka rawar gani wajen tabbatar da yarjejeniyar nukiliya ta shekarar 2015 (JCPOA).

Turjiya

A shekarar 2025, a daidai lokacin da tashe-tashen hankula ke ƙaruwa a yankin, aka sake naɗa Larijani a matsayin Sakataren Majalisar Koli ta Tsaro ta Ƙasa.

Tun farkon yaƙin Amurka da Isra’ila akan Iran, ya zama wanda ke bayyana matsayar kasar ga duniya.

A ranar Juma’ar da ta gabata, an gan shi yana tattaki a zanga-zangar ranar Kudus ta duniya, domin nuna cewa gwamnati tana nan da ƙarfinta.

Kalamansa sun ƙara tsananta bayan mutuwar Ali Khamenei.

“Ba za mu kyale Amurka ba har sai mun dauki fansa kan kisan jagoranmu,” in ji Larijani.

A jajiberin mutuwarsa, ya fitar da sako na hukuma yana kare harin da Iran ta kai kan sansanonin Amurka, inda ya bayyana rikicin a matsayin abin da aka tilasta musu.

“Iran ba ta neman yaki, amma ba za ta ja da baya ba idan aka kakaba mata shi,” in ji shi.

Yayin da yankin ke gab da faɗawa cikin gagarumin yaki, rashin Larijani ya bar babban gibi a cikin kusoshin da ke zagaye da sabon jagoran addinin.