Hukumar gudanarwa ta ƙungiyar Barcelona ta Sifaniya ta sanar da sake zaɓen Joan Laporta, a matsayin wanda zai ci gaba da jagorantar ƙungiyar na tsawon shekaru biyar.
Laporta ya lashe zaɓen da ya gudana ranar Lahadi 15 ga Maris, 2026, inda mambobin ƙungiyar suka kaɗa masa ƙuri’u 32,934, wanda ya ba shi kashi 68.18% na ƙuri’un da aka kaɗa.
Wannan ne karo na huɗu da Joan Laporta zai jagoranci Barcelona, bayan da ya zamo shugaban Barca a 2003, da 2010, da kuma daga Maris ɗin 2021.
Da yake jawabi bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen, Laporta ya ce, "wannan gagarumin sakamako ne kuma ya ba mu ƙwarin gwiwa. Ya mai da mu gagarabadau. Babu wanda zai tsayar da mu. Akwai shekaru masu armashi gaba. Za su zamo mafi kyawu a rayuwarmu.”
“Zan ambaci mambobi na musamman da suka zo suka zaɓe ni. Abu ya kasance bikin dimukuraɗiyya da tsarin jama’a. Kuma zan so na yi nuni kan kyakkyawan aikin da jami’an gudanarwarmu suka yi da sauran jami’ai na shirya wannan ranar zaɓe.”
An haifi Joan Laporta ranar 29 ga Yunin 1962 a garin Barcelona, kuma ya zama shugaba na farko da ya ja ragamar ƙungiyar Barcelona a karo biyu lokuta daban-daban.
Laporta ya karanci fannin shari’a a Jami’ar Barcelona, kuma yana da digiri na biyu a dokokin kamfanoni da haraji daga makarantar Instituto de Estudios Superiores Abat Oliba a Barcelona.
A yanzu shi ɗaya ne cikin mutanan da suka kafa kamfanin lauyoyi na Laporta & Arbós Advocats Associats; kuma shi mamba ne na ƙungiyar lauyoyi ta Barcelona.





