| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Sojojin Benin sun yi ikirarin juyin mulki a Jamhuriyar Benin
Gungun na sojin waɗanda suke kiran kansu, ‘Military Committee for Refoundation’ wato Kwamitin Soja na Sake Gina Ƙasa’, sun sanar da cire shugaban ƙasa mai ci Patrice Talon.
Sojojin Benin sun yi ikirarin juyin mulki a Jamhuriyar Benin
Sojojin sun sanar da Laftanal Tigri Pascal a matsayin sabon jagoran ƙasar. / AFP
7 awanni baya

Wasu sojoji sun bayyana a gidan talabijin na gwamnatin Benin inda suka sanar da rusa gwamnatin ƙasar a abin da ake ganin wani juyin mulki ne, wanda wannan shi ne na baya-bayan nan da aka yi a Yammacin Afirka.

Gungun na sojin waɗanda suke kiran kansu, ‘Military Committee for Refoundation’ wato Kwamitin Soja na Sake Gina Ƙasa’, sun sanar da cire shugaban ƙasa mai ci Patrice Talon.

Haka kuma sojojin sun sanar da Laftanal Tigri Pascal a matsayin sabon jagoran ƙasar.

Sojojin da Laftanal Kanal Pascal Tigri ke jagoranta sun kutsa gidan talabijin na ƙasar da safiyar Lahadi.

Ba a san inda Talon yake ba a halin yanzu. An samu rahotannin harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa.

 ‘Karamin gungun sojoji’

Sai dai, ofishin Shugaba Patrice Talon ya ce yawancin sojojin ƙasar na nan daram suna goyon bayan gwamnatinsa.

Shugaba Talon yana “lafiya” kuma sojoji suna sake karɓar iko, bayan wani rukuni na sojoji ya ce sun kifar da shi, in ji fadar shugaban ƙasa ga kamfnain dillancin labarai na AFP a ranar Lahadi.

“Wannan ƙaramin gungu ne na mutane waɗanda ke riƙe da gidan talabijin kaɗai,” in ji ofishinsa. “Sojojin gwamnati na sake karɓar iko. Birni da ƙasar gaba ɗaya suna cikin tsaro.”

Wannan na faruwa ne a cikin jerin juyin mulki da dama da suka afku a Yammacin Afirka da Afirka ta Tsakiya a ’yan shekarun nan.

A watan da ya gabata, sojoji sun karɓi mulki a Guinea-Bissau, inda suka kifar da Shugaba Umaru Embalo, a daidai lokacin da kasar ke jiran sakamakon zaben shugaban ƙasa mai tayar da kura, wanda yake neman wa’adi na biyu.