| hausa
KASUWANCI
4 MINTI KARATU
Tattalin arzikin Jamus ya shiga mawuyacin hali
Ba za a iya rabuwa da barazanar durkushewar tattalin arziki ba, kuma a yanzu tambayar ita ce ko za a samu ikon farfadowa a watanni shida na karshen shekara?
Tattalin arzikin Jamus ya shiga mawuyacin hali
Iyalai a Jamus sun rage yawan kayayyakin da suke saya da kaso 1.2/ Hoto: Rueters
25 Mayu 2023

A farkon 2023 tattalin arzikin Jamus ya shiga mummunan yanayi na durkushewa – inda iyalai suke gwagwarmaya da tashin gwauron zabi na kayan masarufi.

Kayayyakin da ake samarwa a cikin gida sun ragu da kashi 0.3 a watannin farkon shekara a lokacin da aka yi gyaran farashi, kamar yadda hasashe na biyu daga ofishin kididdiga ya bayyana a ranar 25 ga Mayu.

Wannan ya faru sakamakon karayar tattalin arzikin da aka samu ta kashi 0.5 a wata uku na karshen 2022.

An bayyana fadawa rikicin durkushewar tattalin arzikin a lokacin da aka samu lokuta biyu na matsi a jere.

Alkaluman yawan kayan da Jamus ke Samarwa a Cikin Gida (GDP) na nuna “Alamu marasa kyau bisa mamaki”, in ji Ministan Kudi Christian Lindner a ranar Alhamis din nan.

Ya kara da cewa idan aka kwatanta Jamus da sauran kasashe da suka ci gaba, to za a ga tattalin arzikinta na durkushewa.

Ya ce “Ba na son Jamus ta yi wasa a gasar da za ta janyo mu kaskantar da kawunanmu zuwa matakin karshe.”

Ministan na nufin kawo hasashen da Asusun Lamuni na Duniya, IMF ya yi kan shiga matsin tattalin arziki a Jamus da Birtaniya da wasu kasashen Turai.

“A karkashin nauyin hauhawar farashin kayayyaki, masu sayen kayayyaki a Jamus sun rusuna, suna ta tirjiye tare da tattalin arzikin da ke faduwa”, in ji Andreas Scheuerle, mai nazari d abincike a DekaBank.

Sayen kayayyaki da iyalai ke yi ya ragu da kashi 1.2 bayan hawa da saukar farashi da kuma gyaran lokaci da aka yi. Haka zalika kudaden da gwamnati ke kashewa sun ragu da kashi 4.9.

“Yanayin dumama gari a lokacin sanyi, sake dawowar hada-hadar masana’antu, tare da taimakon sake bude China, da kuma saukin isar da kayayyaki ga jama’a, ba su isar ba don fita daga matsin tattalin arziki”, in ji shugaban ING Carsten Brzeski.

Wani abu da ya sha bam-bam da wannan kuma shi ne yadda zuba jari ya karu a watanni uku na farkon wannan shekarar, bayan raunin da aka samu a watanni shida na karshen 2022.

“Farashin makamashi ya yi tashin gwauron zabi har zuwa tsakiyar sanyi”, in ji shugaban tattalin arziki na bankin Commerzbank.

Ba za a iya rabuwa da barazanar durkushewar tattalin arziki ba, kuma a yanzu tambayar ita ce ko za a samu ikon farfadowa a watanni shida na karshen shekara.

Brzeski na ING ya kara da cewa “Duba zuwa ga sama da watanni uku na farko, fatan da ake da shi a farkon shekara ya kau inda ake fuskantar hakikanin yanayin da ake ciki.”

Raguwar karfin sayen kayayyaki, matse bakin aljihu da gwamnatoci ke yi da kuma tsammanin tafiyar hawainiya da tattalin arzikin Amurka zai yi, duk sun ta’allaka ga muhawara kan hada-hadar tattalin arziki mai rauni.

Sakamakon raguwar hada-hada a yanayin kasuwancin IFO, dukkan alamu a bangaren samar da kayayyaki sun nuna komai na yin kasa, a kalamin Kraemer na Commerzbank.

Amma bankin Bundesbank na Jamus na tsammani da hasashen tattalin arzikin zai habaka a watanni uku na biyu na shekarar nan saboda yadda hada-hada a masana’antu ta dawo, kamar yadda rahoton wata-wata kan tattalin arziki ya fitar a ranar 24 ga Mayu.

MAJIYA:TRT World
Rumbun Labarai
Kamfanin simintin Dangote ya fara aiki a ƙasar Ivory Coast
Ana hasashen mambobin OPEC+ za su ƙara yawan fetur ɗin da suke fitarwa yayin da farashinsa ke karewa
Gwamnatin ƙasar Ghana ta ƙara farashin koko
Nijar ta samu tallafin $145m daga bankin AfDB domin inganta makamashi da tattalin arziki
Elon Musk na dab da zama mutum na farko da arzikinsa ya kai tiriliyan a duniya: rahoto
Dangote zai mai da ma'aikatan Matatar Mai da aka kora daga aiki - Ma'aikatar Ƙwadagon Nijeriya
Kamfanin Orano na Faransa ya ce ya tara tan 1,500 na uranium a Nijar
Kamfanonin haɗin gwiwa ƙarƙashin Saudiyya za su sayi kamfanin wasannin game na Electronic Arts (EA)
Kamfanin Turkish Airlines zai sayi jiragen sama na Boeing 225 bayan Trump da Erdogan sun tattauna
Hukumomi a Ghana sun kama mutanen da ake zargi da yin fasa-ƙwaurin zinari
Matatar mai ta Dangote ta yi watsi da jita-jitar dakatar da aiki na wasu watanni
Babban Bankin Ghana ya dakatar da lasisin cinikin kuɗin ƙetare na UBA da wasu manhajojin aika kuɗi
Farashin ƙwallon kaɗanya ya faɗi warwas a Nijeriya bayan ƙasar ta dakatar da fitar da shi
Babban Bankin Ghana ya ba da sabbin sharuɗɗan kuɗaɗen ƙetare ga masu shiga da kayayyaki
Madogarar bincike kan abincin da aka sauya wa halitta (GMO), da dalilan karɓuwarsa a Nijeriya
Manoman koko a Ghana sun fi takwarorinsu samun farashi mai kyawu a Yammacin Afirka – COCOBOD
Nijeriya na sa ran ganin sakamako mai kyau bayan aiwatar da wani kyakkyawan tsari a harkar kamfanoni
Kamfanin Tsaro na Turkiyya zai ƙulla yarjejeniya da Malaysia don samar mata da motocin yaƙi
Turkiyya da Libya sun kulla yarjejeniyar hakar ma’adanai, samar da makamashi da ababen more rayuwa
Filin jiragen sama na Istanbul ya sake cirar tutar tashin jirage a Turai, in ji Ministan Sufuri