| Hausa
WASANNI
1 MINTI KARATU
Barcelona za ta soma hada-hada a kasuwar hannayen-jarin Amurka
Masu hannayen-jari a cikin Barca Media za su ci gaba da rike kashi 80 cikin 100 daga sashen.
Barcelona za ta soma hada-hada a kasuwar hannayen-jarin Amurka
Katafaren filin wasan kwallo na Barcelona / Photo: AP / AP
11 Agusta 2023

Barcelona ta ce sashen watsa shirye-shiryenta na 'Barca Media' zai sanya hannayen-jari a kasuwar hada-hadar hannun-jari ta Amurka.

Kungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Juma'a.

Barca ta ce za ta hada gwiwa da wani kamfani na musamman wanda ya yi wa jarin kungiyar darajar da ta kai dala biliyan daya.

Sashen watsa shirye-shirye na Barca zai fara hada-hadar kasuwanci a Kasuwar Hannun-Jari ta Nasdaq da ke Amurka bayan kulla wata yarjejeniya da Mountain & Co I Acquisition Corp, a cewar sanarwar Barcelona.

Masu hannayen-jari a cikin Barca Media za su ci gaba da rike kashi 80 cikin 100 daga sashen, idan har ba wanda ya janye jarinsa daga cikin dukka kamfanonin da suka saka hannayen-jari.

MAJIYA:Reuters