Wata gobara ta tashi a jirgin ruwan Amurka na dakon jiragen sama na yaƙi mai suna Gerald R Ford yayin da yake aiki a Gabas ta Tsakiya a wani ɓangare na yaƙin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran ta sa jami’ai fiye da 600 sun rasa gadaje , in ji wani rahoto da jaridar New York Times ta ruwaito ranar Litinin.
Gobarar ta tashi ne a ɗakin wanki na jirgin ruwan a makon jiya, kuma jami’an soji sun ce ma’aikatan jirgin sun shafe sa’o’i 30 kafin su iya kashe ta.
Gomman jami’ai ne aka ba da rahoton cewa sun gamu da iftila’in shaƙar hayaƙi kuma biyu daga cikinsu sun samu kulawa sakamakon jin ciwo na wani “yanayi mara barazana ka rayuwa".
Jami’an jirgin da suka rasa gadajensu suna kwana ne a ƙasa da kan tebura, kuma tun da wutar ta samo asali ne daga ɗakin wanki, sojoji masu tuƙin jirgin ruwa ba su da yadda za su wanke kayayyakinsu.
Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya bai wa jirgi mai dakon jiragen yaƙin, tare da sojojin ruwa masu tuƙin jirgin ruwanta 4,500 da kuma masu tuƙa jiragen sama na yaƙi, umarnin barin tekun Mediterranean zuwa na Caribbean ranar 24 ga watan Oktoba.
Umarnin wani ɓangare ne na tara dakarun Amurka wanda aka yi domin ƙara matsin lamba kan shugaban Venezuela Nicolas Maduro kafin a kama shi a farkon watan Janairu.
Daga baya jirgin ruwan ya nufi Gabas ta Tsakiya domin yaƙin Amurka da Isra’ila kan Iran, wanda a halin yanzu ya shiga mako na uku.
Gaba ɗaya, jami’an kan jirgin ruwan sun shiga watansu na 10 da suka fita aiki, kuma idan jirgin ya kai tsakiyar watan Afrilu a cikin teku, zai kafa tarihi na jirgin da ya fi daɗewa a aiki tun bayan yaƙin Vietnam.
Tun da jami’an kan jirgin sun ce an shaida musu cewa fita aikinsu zai iya kai zuwa watan Mayu, za su zarta tarihin kwanaki 294 a teku da jami’an jirgin USS Abraham Lincoln suka kafa a shekarar 2020.
Hedkwatar ba da umarnin sojin Amurka ta tsakiya ta bayyana a wata sanarwa cewa wutar " ba ta lalata ɗakin tuƙin jirgin ba kuma jirgi mai dakon jiragen yaƙin yana aiki ɗari bisa ɗari," amma jami’an kan jirgin sun ba da rahoton cewa tsarin fulomban bayi 650 na kan jirgin suna ɓaciwa sau da yawa.
"Jiragen ruwa ma suna gajiya, kuma suna ɓacewa idan aka tura su aiki inda suka daɗe," in ji Rear Adm John F Kirby, wani sojin ruwa mai murabus kuma sakataren watsa labaran Pentagon a gwamnatin Shugaba Biden, inda ya shaida wa the Times cewa. "Babu yadda za ka yi aiki da wani jirgin ruwa na irin wannan lokacin mai tsawo kuma sosai haka kuma ka yi tsammanin cewa jirgin ko jami’ansa za su sosai yadda ya kamata."
Duk da koma baya na baya bayan nan daga gobarar, jirgi mai dakon jiragen yaƙin yana aiwatar da tashi da sauƙar jirage babu ƙaƙƙautawa, in ji jami’an sojin ruwa.









