| hausa
AFIRKA
4 MINTI KARATU
ECOWAS na buƙatar dala biliyan 2.6 duk shekara don kafa rundunar tsaro - Ministan Tsaro Nijeriya
Ministocin Tsaro da na Kuɗi na Ƙasashen ECOWAS sun yi ganawar a Abuja, babban birnin Nijeriya, inda suka tattauna kan yanke shawarar yawan dakarun da ake buƙata da kuma yawan kuɗaɗen da ake buƙata don samar da rundunar tsaron yanki.
ECOWAS na buƙatar dala biliyan 2.6 duk shekara don kafa rundunar tsaro - Ministan Tsaro Nijeriya
Ministan Tsaron Nijeriya ya kara da cewa ba za a yi amfani da rundunar yankin wajen ɗaukar mataki a kan juyin mulkin ba, illa kawai yaƙi da ta'addanci. Hoto: Badaru X.
27 Yuni 2024

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS tana buƙatar dala biliyan 2.6 duk shekara don samar da ƙaƙƙarfar rundunar tsaro da za ta yi yaƙi da ta’addanci, a cewar ɗaya daga cikin zaɓuka biyun da hukumomin tsaro na ƙasashen yankin ke duba yiwuwarsu a taron da suka yi a yau Alhamis.

Ministocin Tsaro da na Kuɗi na Ƙasashen ECOWAS sun yi taron a Abuja, babban birnin Nijeriya, inda suka tattauna kan yanke shawarar yawan dakarun da kuma yawan kuɗaɗen da ake buƙata don samar da ita.

Afirka ta Yamma na fama da matsalolin juyin mulki, lamarin da yake zama matsala ga tsarin siyasa da jawo rarrabuwar kai tsakanin ƙasashen yankin.

A watan Janairu, shugabannin mulkin soji na Nijar da Burkina Faso da Mali sun yanke shawarar ficewa daga ƙungiyar mai mambobin ƙasashe 15.

Ministan Tsaron Nijeriya ya shaida wa taron cewa akwai zaɓi biyu a samar da rundunar yankin: Daya za a kashe dala biliyan 2.6 duk shekara a kan runduna mai dakaru 5,000, dayan kuma za a kashe dala miliyan 481 a dakaru 1,500

“Wadannan alkaluma sun nuna muhimmancin aikin da ke gabanmu,” in ji Badaru. "Don haka ya zama wajibi mu yi nazari sosai kan zabin duba da irin kalubalen da yankinmu ke fuskanta a halin yanzu da kuma matsalolin kudi da kasashe mambobinmu ke fuskanta."

Tun a shekarar 2020, sojoji a kasashen uku suka yi juyin mulki suna zargin shugabannin farar hula da ƙyale masu da'awar jihadi su samu galaba.

Da hawansu kan mulki, sojojin sun yi watsi da yarjejeniyoyin tsaro da aka ƙulla da sojojin Amurka da Faransa da kuma na Majalisar Dinkin Duniya tare da gayyatar Rasha da su maye gurbinsu.

Ministan Tsaron Nijeriya ya kara da cewa ba za a yi amfani da rundunar yankin wajen ɗaukar mataki a kan juyin mulkin ba, illa kawai yaƙi da ta'addanci. Ana sa ran kowace ƙasa mamba za ta ba da gudunmawar wani kaso, in ji shi.

Shugaban hukumar ECOWAS Omar Touray ya ce ba za a cire mambobin da aka dakatar daga cikin rundunar yankin ba.

"An yi imanin ba za mu iya yaki da ta'addanci mu kadai idan har wasu ba su shiga ba," in ji Touray.

"Ko da yake ana iya dakatar da wasu kasashe amma ya kamata a bar su su shiga tarukan da suka shafi tsaro, shi ya sa muka gayyaci dukkan kasashe mambobi 15 da su halarci wannan muhimmin taro."

MAJIYA:Reuters
Rumbun Labarai
An samu rahotanni 32 na yi wa 'yan mata fyade bayan RSF ta ƙwace birnin Al Fasher - Likitoci
Mutum huɗu sun rasu bayan jiragen ruwa biyu na 'yan ci-rani sun kife a gaɓar tekun Libya
DR Congo da M23 sun cim ma yarjejeniyar zaman lafiya 'ta tarihi' a Qatar
AfDB zai ba Nijar CFA biliyan 98.7 domin magance matsalar ruwa ta shekara 70 a Zinder
MDD ta yi gargaɗi kan ƙazancewar yaƙin Sudan, ta yi kira kan barin shigar da kayan agaji
An gabatar da GH¢302bn a matsayin kasafin kuɗin Ghana na 2026 ga majalisar dokokin ƙasar
Sojojin Sudan sun daƙile harin RSF kan filin jirgin sama da dam a arewacin ƙasar
Rubio ya nemi a daina bai wa RSF makamai, ya ɗora wa rundunar laifi kan kashe-kashe a Al Fasher
Dalilin da ya sa TikTok ya goge bidiyoyi miliyan 1.5 da 'yan Uganda suka wallafa
Mutum 12 sun mutu a turmutsutsun neman aikin soja a Ghana – Rahotanni
Mahaucin Al Fasher: Yadda hotonsa ya zama alamar bakin cikin Sudan
UN Women: Mata da 'yan mata 11M suna fama da matsanancin ƙarancin abinci a Sudan sakamakon yaƙi
WHO ta bayyana damuwa kan karuwar masu ciwon siga a Afirka
Kisan kare dangi a boye da bayyane: Gushewar jinkai a Al Fasher
An ba da belin dan Gaddafi bayan da ya shafe shekaru 10 a tsare a Lebanon
Gwamnatin Trump 'ta aika wa Equatorial Guinea dala miliyan 7.5' don ta karɓi waɗanda Amurka ta kora
Ƙasashe fiye da 20 sun yi Allah wadai da RSF kan kashe-kashen da take yi a Sudan
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi kira da a dakatar da zubar da jini a Sudan
Paul Biya na Kamaru: Dan siyasar da zai ci gaba da yin mulki har sai ya kai shekara 99?
Hare-haren RSF sun kori ƙarin dubban mutane daga Darfur da Kordofan na Sudan