| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Sojojin Isra'ila sun yi kisa cikin ruwan sanyi a Jenin, Falasɗinawa sun ambace shi laifin yaƙi
Ministan Tsaron Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi Ben-Gvir ya fitar da sanarwa yana bayar da "cikakken goyon bayansa" ga sojoji da 'yan sandan da suka aikata "laifin yakin."
Sojojin Isra'ila sun yi kisa cikin ruwan sanyi a Jenin, Falasɗinawa sun ambace shi laifin yaƙi
Jami'an Falasdinawa sun ce sojojin Isra'ila sun kashe samari biyu kisan gilla.
6 awanni baya

Hukumomin Falasɗinu sun zargi rundunar sojin Isra'ila da aikata 'laifin yaki' da gangan, bayan wani mummunan kisan da aka yi wa mutane biyu cikin ruwan sanyi a Jenin, a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da ake mamaye.

Ma'aikatar harkokin wajen da ke Ramallah ta bayyana a ranar Alhamis cewa ta yi kakkausar suka ga wannan kisan gillar da sojojin mamayar Isra'ila suka yi wa matasa Falasɗinawa biyu, ta kuma kira lamarin 'laifin yaki da sra'ila ta aikata da gangan'.

Wasu bidiyoyi da tashar Palestine TV ta wallafa sun nuna sojojin Isra'ila suna harbe maza Falasɗinawa biyu wadanda ba su dauke da makami a ranar Alhmis .

A cikin bidiyon, an ga mazan suna fita daga wani gini da sojojin Isra'ila suka yi wa ƙawanya a garin Jenin, arewacin Yammacin Kogin Jordan da aka mamayem suna daga rigunansu sannan suka kwanta a kasa.

Bidiyon ya nuna alamar sojojin suna ta tilasta musu komawa cikin ginin kafin su bude musu wuta a kusa da su.

Wani dan jaridar Reuters da ke kusa ya ga mutanen suna barin ginin, kamar suna mika wuya, sannan daga baya, bayan jin harbe-harbe, ya ga sojojin Isra'ila suna tsaye kusa da abin da ya bayyana a matsayin jiki mara rai.

A cikin wata sanarwa ma'aikatar kiwon lafiya ta Palasɗinu ta ce an kashe mutanen biyu yayin harbin, ta kuma bayyana su a matsayin Montasir Abdullah mai shekaru 26 da Yusuf Asasa mai shekaru 37.

Gwamnan Jenin Kamal Abu al-Rub, ya zargi sojojin Isra'ila da yin kisan gilla ba tare da tausayin matasa biyu ba.

Ya ce ya kamata wadanda suka bude wutar su fuskanci hukunci, amma ya nuna shakku cewa hukumomin Isra'ila za su yi sahihin bincike.

Ministan Tsaron Israel mai tsattsauran ra'ayi Ben-Gvir ya fitar da sanarwa inda ya ce yana bayar da "cikakken goyon bayansa" ga sojoji da 'yan sandan da suka aikata "laifin yakin."