A ranar Juma'a ne aka fara taron Yaki da Shara a Istanbul, wanda Gidauniyar Yaki da Shara ta shirya, wanda aka ƙaddamar a ƙarkashin jagorancin uwargidan shugaban kasar Turkiyya Emine Erdogan, da Ma'aikatar Kula da Muhalli, Birane da Sauyin Yanayi, da Ma'aikatar Noma da Gandun Daji.
Erdogan ce ta kirkiri shirin, wadda kuma ita ce shugabar Kwamitin Ba Da Shawara kan Yaki da Shara na Majalisar Dinkin Duniya, kuma shugabar Gidauniyar, tare da hadin kan MDD.
An gudanar da taron ne a karon farko a wannan shekara, karkashin taken "Mutane, Wurare, Ci gaba."
Muhimman wuraren da za a mayar da hankali a kai su ne ɗabbaka manufofi a aikace, daidaita mafita, tattara kudi, da kulla ƙawance.
A yayin taron na kwanaki uku, tare da mahalarta daga kasashe 104 da abokan huldar kasa da kasa 118, bangarorin za su binciko jigogi kamar ma'anar yaki da shara, ka'idoji, kudi, makomar tufafi, sake amfani da su, tasirin ƙirkirarriyar basira, fasaha, da mafita.
Guy Bernard Ryder, mataimakin babban sakataren MDD mai kula da manufofi, a madadin Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, na daga cikin mahalarta taron, tare da Babbar Daraktar MDD kan muhalli Anaclaudia Rossbach, da kuma wakilin Shugaban Kasar Azarbaijan na musamman kan harkokin yanayi Mukhtar Babayev.
A ranar Lahadi ne za a kammala taron wanda ya samu halartar Ministan Muhalli na kasar Turkiyya Murat Kurum da Ministan Noma da Gandun Daji Ibrahim Yumaklı.
An kafa gidauniyar Yaki da Shara a shekarar 2023 a karkashin Uwargidan Shugaban Kasar Turkiyya. Ƙungiyar na aiki don inganta aikin Yaki da Shara da tabbatar da dore war muhalli. Tun lokacin da aka kafa ta, ta kasance tana aiki tare da kwamitin ba da shawara na Sakatare-Janar din Majalisar Dinkin Duniya.