TURKIYYA
2 minti karatu
Tsarin duniya na yanzu ya fi ba da fifiko kan iko fiye da adalci: Babban Daraktan TRT Sobaci
An fara taron duniya na TRT World karo na tara a Istanbul, inda ka haɗa shugabanni da manazarta da masu kawo sauyi daga sassan duniya.
Tsarin duniya na yanzu ya fi ba da fifiko kan iko fiye da adalci: Babban Daraktan TRT Sobaci
Babban daraktan TRT Mehmet Zahid Sobaci ya yi kira da a samar da wata sabuwar manufa ga tsarin duniya / AA
16 awanni baya

Babban daraktan TRT Mehmet Zahid Sobaci ya yi kira da a samar da wata sabuwar manufa ga tsarin duniya, yana mai cewa tsarin iko na duniya ya fi ba da fifiko kan fin ƙarfi na siyasa da soji fiye da halin kirki da adalci.

Da yake magana da taron duniya na TRT na shekarar 2025 da ake yi a Istanbul ranar Jumma’a, Sobaci ya ce tsarin duniya na yanzu ba zai iya warware rikice-rikice da ke ƙaruwa a duniya ba domin “an fi ba da fifiko kan iko fiye da hali na gari.”

“Tsarin duniya na yau ba zai iya samar da mafita ga matsalolin da take fuskanta ba,” kamar yadda ya bayyana wa wakilan taron.

“Muna buƙatar wata sabuwar manufa domin mu iya gina wani tsarin duniya da ya fi adalci bisa doka da kuma tsari na duniya mai hali na gari.”

Da yake magana game da tauye haƙƙin bil’adama da ake yi, Sobaci ya yi Allah wadai da ƙoƙarin da ake yi na  halasta kisan ƙare-dangin Isra’ila a Gaza cikin shekaru biyun da suka gabata, yana mai jaddada cewa Turkiyya ta ci gaba da tsayawa tsayin daka a matsayin muryar adalci domin kare waɗanda ake yi wa danniya da rashin adalci.

“Cikin shekaru biyun da suka wuce, an yi ƙoƙari  halasta kisan ƙare-dangin Isra’ila a Gaza,” a cewarsa.

“Amma Turkiyya ta kasance muryar adalci.”

“Yayin da duniya take kallon halaka wasu mutane babu ƙaƙƙautawa, Turkiyya ba ta yi shiru ba,” in ji shi.

An fara taron TRT World na duniya karo tara a Istanbul, inda aka haɗa shugabanni da manazarta da masu kawo sauyi daga sassan duniya domin tattauna yada ake sake sauya yadda duniya take a lokacin rashin tabbas.

Taron da ake yi da taken "Sake fasalin Duniya: Daga tsohon tsarin duniya zuwa sabbin ababen da ke wakana", taron na kwanaki biyu yana nazari game da yadda sauyi a tattali arziƙi da fasaha da da kafafaen watsa labarai da kuma dokokin ƙasa da ƙasa suke sake fasalin duniyar da muke rayuwa a cikinta.

Taron da kafar watsa labaran ƙasar Turkiyya TRT, taron na shekara shekara ya kasance wani wuri na kawo batutuwan da ba a magana a kansu gaba-gaba da kuma ƙalubalantar rawar da kafafan watsa labarai ke takawa wajen sauya labaran duniya.