An kammala taron kasuwanci da tattalin arziki na biyar tsakanin Turkiyya da Afirka (TABEF) a ranar Jumma’a a Istanbul, inda aka kara karfafa daya daga cikin kawance mafi tasiri tsakanin kasashen kudancin duniya.
Taron, wanda aka gudanar karkashin taken “Amfani da Dangantakar Turkiyya da Afirka don Amfanin Juna,” ya tara fiye da mahalarta 4,000, ciki har da shugabannin kasashe, ministoci, jakadun kasashen waje, da shugabannin bangaren masu zaman kansu daga nahiyar Afirka da Turkiyya.
A cikin daya daga cikin jawabai mafi jan hankali a taron, Francisca Tatchouop Belobe, Kwamishinan Kungiyar Tarayyar Afirka mai kula da Ci gaban Tattalin Arziki, Yawon Bude Ido, Kasuwanci, Masana’antu, da Ma’adinai, ta bayyana kawancen Turkiyya da Afirka a matsayin “bai tsaya kan gaskiya ba kawai ba, amma wanda ya yi nisan da ba ya jin kira”.
Jawabinta ya nuna karuwar fahimtar juna tsakanin shugabanni cewa wannan kawance ba kawai yana tasowa ba ne, amma yanzu ya tabbata kuma yana sake fasalin yadda kasashen kudancin duniya ke gudanar da kasuwanci.
‘Abokiyar Amana’
“Turkiyya ba bakuwa ba ce a wannan tafiya,” in ji Kwamishina Belobe. “Abokiyar amana ce, tana gina, zuba jari, sauraro, da aiki tare da burin Afirka.”
Kwamishinar ta bayyana ci gaban tattalin arziki mai ban mamaki a jawabinta. “A cikin shekaru fiye da ashirin kacal, cinikayya tsakanin Afirka da Turkiyya ta karu daga dala biliyan 4.5 a shekarar 2003 zuwa fiye da dala biliyan 40.7 a shekarar 2024,” in ji ta.
Wannan ci gaba mai ban mamaki ya sanya Turkiyya cikin manyan abokan cinikayya guda biyar na ƙasashen da ba na Afirka ba a nahiyar. Tare da burin cim ma dala biliyan 50 nan da shekarar 2026, Belobe ta lura cewa karfin wannan dangantaka ba kawai tana da karfi ba ne, amma tana kara karuwa.
“Muna ganin dangantakar da aka gina bisa ga kudurin siyasa da burin bangaren masu zaman kansu,” in ji ta. “TABEF hujja ce cewa wannan ba kawai diflomasiyya ba ce — amma aiki ne.”
Fiye da Adadin Cinikayya
Zuba jarin Turkiyya a Afirka yana nuna tsanaki da zurfin dangantaka. Zuba Jarin Kai Tsaye na Wajen Turkiyya (FDI) ya zarce dala biliyan 8.5, yana tallafa wa ayyuka a bangarori kamar makamashi mai sabuntawa, dabarun dijital, masana’antu, gine-gine, da sauransu.
Fiye da kamfanoni 1,500 na Turkiyya ke aiki a Afirka, galibi suna yin hadin gwiwa kai tsaye da kananan masana’antu da cibiyoyi na cikin gida.
“Turkiyya tana zuba jari ba don amfani kawai ba, amma don sauyi,” in ji Belobe. “Tana tallafa wa kananan masana’antu, tana raba fasaha, tana samar da kwarewa, wannan shi ne hangen nesa na dogon lokaci a aikace.”
Yawancin wadannan kawance sun bayyana a yankin baje-kolin taron, inda Belobe ta gana da ‘yan kasuwa da masu kirkira daga nahiyar. Ta jaddada wani kamfani na Afirka da ke amfani da fasahar wucin-gadi don sauya dabarun, da wani kamfani na Turkiyya da ke kirkirar hanyoyin makamashi mai dorewa a karkarar Afirka.
“Wadannan ba labarai ne kawai ba. Hujjoji ne,” in ji ta. “Wannan shi ne yadda kawance na karni na 21 yake — kirkira tare da amfanin juna.”
Afirka, ta jaddada, ba kawai tana bude kasuwanci ba ne, amma tana tsara makomar kasuwancin kanta. A shekarar 2024, nahiyar ta jawo dala biliyan 97 na zuba jari kai tsaye, wanda ya wakilci karin kashi 7.5% daga shekarar da ta gabata.
Cinikin cikin Afirka ya karu zuwa dala biliyan 280, kuma kasashe 15 sun samu karuwar ma’aunin GDP na fiye da kashi 5%, duk da kalubalen duniya.
Amfanin Yawan Jama’a na Afirka
Mafi muhimmanci, amfanin yawan jama’a na Afirka yana daya daga cikin manyan kadarorinta. Tare da matsakaicin shekaru na 19.5 kacal da yawan jama’a da ake sa ran zai kai biliyan 2.5 nan da shekarar 2050, nahiyar tana da mafi girman adadin matasa, kirkira, da bukatu a duniya.
“Nan da shekarar 2030, kashi 43% na matasan duniya za su kasance ‘yan Afirka,” in ji Belobe. “Mu ne nahiyar da ta fi kowacce matasa — kuma wadannan matasa su ne kuzari, buri da makoma,” kamar yadda ta bayyana.
Tsarin Cinikayya na Marsa Shinge na Afirka (AfCFTA) - wani muhimmin shiri karkashin Ajandar AU ta 2063, shi ma ya kasance a matsayin ginshikin sauyin tattalin arzikin nahiyar.
Tare da kimanin darajar dala tiriliyan 6.7 nan da shekarar 2035, AfCFTA na shirin zama kasuwar ciniki guda mafi girma a duniya. Belobe ta yaba da goyon bayan Turkiyya ga ajandar cinikayya ta nahiyar, tana mai lura da cewa kudurin Ankara ya wuce yarjejeniyoyin bangarori biyu zuwa tallafa wa hadewar yankuna.
“Turkiyya ta fahimci cewa karfin Afirka yana cikin hadin kanta; gine-ginen iyaka, da dokokin cinikayya masu daidaito,” in ji ta.
TABEF, wanda aka gudanar a Cibiyar Taro ta Istanbul, ya kasance fiye da taron al’ada. Wuri ne da aka tattauna yarjejeniyoyi, aka sanar da kawance, kuma aka tsara bangarori don zuba jari a nan gaba. An tattauna batutuwa daga makamashi maras gurɓata muhalli zuwa kayan aikin dijital, inda ake kallon Turkiyya a matsayin abar dogaro wurin zuba jari.