WASANNI
2 minti karatu
Kotu ta umarci Barcelona ta fito da takardun biyan dala miliyan 9 ga wani rafari
Wata kotu a garin Barcelona na Sifaniya ta umarci mahukuntan ƙungiyar Barcelona da su fito da takardun kwantiragin da aka biya alƙalin wasa Negreira dala miliyan 9 da aka ce sun ɓata.
Kotu ta umarci Barcelona ta fito da takardun biyan dala miliyan 9 ga wani rafari
An biya dala miliyan 9 ne ga Jose Maria Enriquez Negreira da wasu kamfanoninsa tsakanin 2001 da 2018. / AP
14 awanni baya

Matsalolin shar'i’a na ci gaba da rincaɓe wa Barcelona, yayin da wata kotun Sifaniya ta umarci ƙungiyar ta kawo kwafin ainihi na kwantiragin da ke da alaƙa da kuɗaɗen da ta biya wani tsohon alƙalin wasa.

An biya rafari Jose Maria Enriquez Negreira, dala miliyan 9 shi da wasu kamfanoni masu alaƙa da shi tsakanin 2001 da 2018.

Umarnin kotu na zuwa ne sakamakon binciken da ake ci gaba da yi kan takardun da suka ɓata, yayin da masu bincike ke neman tantance ko kuɗaɗen na halal ne ko kuma da manufar yin tasiri kan alƙalanci.

Batun da ake wa laƙabi da Badakalar Negreira ta zamo ɗaya cikin jerin manyan takaddamar shari’a a Sifaniya fannin ƙwallon ƙafa.

Lamarin na ƙara dagulewa ne yayain da masu bincike suka gaza gano takardun ainihin na kwantiragin, ko wani rubutaccen bayani a ma’ajiyar Barcelona da ke nuna hujjar biyan kuɗaɗen.

A zahiri dai an nuna cewa kuɗin na “shawarwari ne kan alƙalancin wasa”. Amma rashin gano takardun ya zafafa zarge-zarge kan yanayin alaƙar Barcelona da tsohon mataimakin shugaban ƙungiyar Alƙalan Wasan Sifaniya.

A halin yanzu dai, kotun ta ba da sammacin Barcelona ta bayyana gabanta don amsa tambayoyi kan lamarin, tare da tsaffin kociyoyin ƙungiyar, Luis Enrique, Ernesto Valverde, da shugaban ƙungiyar Joan Laporta.