Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sake jaddada aniyarta ta yaƙi da tsattsauran ra’ayi wanda ta ce wasu masu son rai ne ke da hannun wurin rura wannan wutar.
Wannan na zuwa ne bayan Amurka ta ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake yi wa Kiristoci kisan gilla.
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta Nijeriya ta fitar a ranar Asabar, gwamnati ta ce tana da cikakken kudiri wajen yakar tsattsauran ra’ayi da ‘yan ta’adda, wanda ta bayyana cewa wasu kungiyoyi masu son zuciya ne ke haifar da shi don raba kawunan al’umma da tayar da hankula a yankin Yammacin Afirka da Sahel.
“Mun kuduri aniyar yakar tsattsauran ra’ayi wanda wasu ke amfani da shi wajen kawo rarrabuwar kawuna da lalacewar al’umma,” in ji sanarwar.
Gwamnatin ta yi jaje ga duk wanda ya rasa rayuwarsa sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda, tare da yaba wa dakarun sojojin Nijeriya saboda jajircewarsu wajen kare ƙasar daga makiya.
“Muna juyayin wadanda suka mutu sakamakon tsattsauran ra’ayi, tare da girmama dakarunmu masu kwazo wajen yaki da makiya marasa imani,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa bambancin addini, kabila da al’ada shi ne karfin Nijeriya.
Ma’aikatar ta kuma jaddada kyakkyawar dangantaka tsakanin Najeriya da Amurka, tana fatan hadin gwiwar kasashen biyu zai ci gaba da karfafa zaman lafiya da dimokiradiyya a duniya.









