| Hausa
WASANNI
3 minti karatu
Dubban mutane sun halarci bikin karrama Zakarun Kofin AFCON a Senegal
'Yanwasa da masu horarwa sun nuna kofin ga jama'a daga saman buɗaɗɗiyar bas wadda ta yi rangadi tsakanin dubban mutane a cikin babban birnin Senegal.
Dubban mutane sun halarci bikin karrama Zakarun Kofin AFCON a Senegal
Senegal ta lashe Kofin Nahiyar Afirka bayan ta doke Morocco mai masaukin baki da ci 1-0 a wasan karshe mai zafi a Rabat ranar Lahadi. / Reuters
21 Janairu 2026

Dubban masoya ƙwallon ƙafa a Senegal sun cika titunan birnin Dakar a ranar Talata, yayin da tawagar “Zakunan Teranga” suka gudanar da faretin murnar nasararsu a wasan ƙarshe na Gasar Kofin Afirka, AFCON 2025.

'Yanwasa da masu horarwa sun nuna kofin ga jama'a daga saman buɗaɗɗiyar bas wadda ta yi rangadi tsakanin dubban mutane a cikin babban birnin Senegal, kuma suka ɗunguma fadar shugaban ƙasa.

Yayin da ‘yanwasan ke kan ƙarshen faretin nasu kusa da titin bakin teku mai suna Corniche, magoya baya sun yi tattaki, wasu kuma sun yi gudu kusa da motar, yayin da wasu suka tsaya kallon ta a gefen hanya.

Shugaban Senegal ya taya tawagar murna kan nasararsu mai cike da tarihi, inda suka doke Maroko a wasan ƙarshe, duk da cewa Marokon ce mai masaukin baƙi.

A filin taron, Shugaba Bassirou Diomaye Faye ya gaya wa ‘yanwasan cewa, sun "nuna jajircewa ta musamman, juriyar ban mamaki, da ƙarfin gwiwa kamar ƙarfe, kuma wannan ya sa nasararku ta zama mai tarihi".

Cibiyar garin ta cika da hayaniya mai yawa da ƙarar injinan motoci da ababen hawa, da kururwar abin busan na mai suna kururuwan vuvuzela, yayin da ‘yanwasan suka kusa isa fadar inda za a karɓe su a hukumance.

Dubban mutane sun taru a wurin gangamin da ya fara a Patte d'Oie, unguwar masu aiki a wani ɓangare na birnin Dakar, suna sanye da rigunan ƙungiyar ƙwallon, suna rera waƙoƙi, suna busa vuvuzela.

A ko’ina a hanyar, manya da yara, maza da mata sun fito sanye da launukan ƙasa na kore, rawaya da ja, wani lokaci suna kallo daga gine‑gine da gadar titi, ko ma hawa kan motoci da allunan talla.

Jami’an tsaro da yawa sun kasance a wurin, ciki har da rukunin 'yan sanda masu tarwatsa zanga‑zanga.

Tawagar Senegal ta yi hanyarta a cikin birnin bayan ta iso ta jirgi na musamman daga Maroko dab da tsakar daren Litinin, inda Shugaba Bassirou Diomaye Faye, Firaminista Ousmane Sonko, da sauran jami’an gwamnati suka tarbe su.

Senegal ta ci Kofin AFCON bayan doke mai masaukin baƙi Maroko da ci 1-0, a wata fafatawa mai cike da hargitsi a birnin Rabat ranar Lahadi, inda zakarun suka bar filin wasa cikin fushi a ƙarshen wasa.

"Ba zan bari in rasa wannan lokacin ko da an ba ni duniya ba," in ji wani masoyin ƙwallo mai shekaru 26, Doudou Thiam, daga gefen gangamin a unguwar Bourguiba, yana mai sanye da rigar tawagar Senegal.

"Tawagar “Zakunan Teranga” su ne abin alfaharin mu, kuma sun cancanci dukkan girmamawa. Ko da hakan zai sa in tsaya a nan duk rana, zan yi," in ji shi.

Wannan nasara ta kasance ta biyu ga Senegal, bayan nasarar da suka samu a 2022 kan Masar a Kamaru. Ita ce karo na uku da suka kai wasan ƙarshe a gasanni huɗu na baya‑bayan nan.