Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jaddada matsayin ƙasarsa na zage dantse wajen bayyana gaskiyar abubuwan da ke faruwa a Gaza tare da tabbatar da ganin “an yi adalci” a lamuran yankin.
"Turkiyya za ta ci gaba da fafutuka bisa ƙwarin gwiwa ta kowace fuska domin ganin ba a manta da abubuwan da ke faruwa a Gaza ba tare da tabbatar da ganin an yi adalci,” in ji Erdogan a jawabin da ya gabatar ranar Alhamis a wajen bikin karramawa kan al’adu da fasaha a babban birnin ƙasar Ankara.
"A matsayinmu na ƙasa da kuma gwamnati da ba ta shayin faɗar gaskiya, Turkiyya za ta ci gaba da yin tsayin-daka wajen goyon bayan al’ummar Falasɗinu ba tare da gajiyawa ba," a cewar shugaban ƙasar.
‘Jaruman’ kafofin watsa labarai
Kazalika Erdogan ya jinjina wa kafofin watsa labaran Turkiyya waɗanda ya bayyana a matsayin “gwaraza” wajen bayar da labarai na gaskiya game da abubuwan da ke faruwa a Gaza.
"A yayin da ake kisan ƙare-dangi a Gaza, kafofin watsa labaran Turkiyya, musamman TRT da Anadolu, sun ɗauki matakai na jarumta," in ji shugaban Turkiyya.
Da yake yaba wa ɗan jarida mai ɗaukar hoto na Anadolu Ali Jadallah, Erdogan ya ce: “Abubuwan da kyamararsa take ɗaukar ba kawai abubuwan tashin hankali game da kisan gillar Gaza ba ne har ma da tirjiya da al’ummar Falasɗinu suke yi domin jawo hankalin al’ummar duniya.”
“Ɗan’uwanmu Ali, wanda ya fallasa kisan ƙare-dangin da ake yi a Gaza tare da nuna gaskiya ga ƙasashen duniya masu iƙirarin wayewa, ɗanjarida ne mai ɗaukar hotuna ga kamfaninnmu na Anadolu," a cewarsa.

















