Kusan ’yan Nijeriya miliyan 35 na fuskantar barazanar yunwa a bana, ciki har da yara miliyan uku da ke fama da mummunar rashin abinci mai gina jiki, in ji Majalisar Ɗinkin Duniya a ranar Alhamis, biyo bayan rasa tallafin kuɗi na ayyukan jin ƙai da ta yi.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da shirin agajin jin-ƙai na shekarar 2026 a Abuja, Mai Kula da MDD a Nijeriya kuma Mai Tsara Ayyukan Agaji, Mohamed Malick Fall, ya ce tsarin taimakon da ƙasashen waje ke jagoranta wanda ya daɗe ana amfani da shi a Nijeriya ba zai ƙara dorewa ba, kuma bukatun Nijeriya sun ƙaru sosai.
Fall ya ce halin da ake ciki a Arewa maso Gabas da rikici ya shafa ya yi muni ƙwarai, inda fararen-hula a jihohin Borno, Adamawa da Yobe ke fuskantar ƙaruwa a tashin hankali.
Ya ce ƙaruwar hare-haren ƙunar baƙin-wake da hare-hare masu yawa sun kashe fiye da mutane 4,000 a cikin watanni takwas na farkon shekarar 2025, adadin da ya yi daidai da jumullar dukka na shekarar 2023.
MDD ta ce za ta iya bayar da dala miliyan 516 ne kacal don bayar da agajin ceto rayuka ga mutane miliyan 2.5 a bana, adadin da ya ragu daga mutane miliyan 3.6 a 2025, wanda shi ma kusan rabin adadin shekarar da ta gabata ne.
“Waɗannan ba ƙididdiga kawai ba ce. Waɗannan lambobi suna wakiltar rayuka, makoma da ’yan Nijeriya,” in ji Fall.
Ya kuma ce UN ba ta da wani zaɓi illa ta mayar da hankali kan agajin da ya fi ceton rayuka, sakamakon raguwar kuɗaɗen tallafi da ake samu.
Rashin isasshen kuɗi a bara ya sa Shirin Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ya yi gargaɗi cewa miliyoyin mutane na iya fuskantar yunwa a Nijeriya, bayan kuɗaɗensa sun ƙare a watan Disamba kuma aka tilasta masa rage tallafi ga fiye da yara 300,000.
Fall ya ƙara da cewa Nijeriya na taimakawa sosai wurin magance matsalolin da ake fuskanta a ‘yan watannin nan ta hanyar ɗaukar matakai waɗanda suka haɗa da bayar da tallafin abinci da kuma yin gargaɗi da wuri a kan batun ambaliyar ruwa.




















