GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Bayanai na hukuma sun nuna cewa sojojin Isra'ila sun yi yunkurin kashe kansu sau 279 cikin wata 18
Bayan rahoton Knesset ya nuna cewa sojojin Isra'ila 36 sun kashe kansu tsakanin Janairun 2024 da Yuli 2025.
Bayanai na hukuma sun nuna cewa sojojin Isra'ila sun yi yunkurin kashe kansu sau 279 cikin wata 18
Bayan rahoton Knesset ya nuna cewa sojojin Isra'ila 36 sun kashe kansu tsakanin Janairun 2024 da Yuli 2025. / Reuters
29 Oktoba 2025

Jimillar sojojin Isra'ila 279 sun yi ƙoƙarin kashe kansu a cikin watanni 18 da suka gabata yayin da Tel Aviv ke yaƙi da Gaza, kamar yadda bayanan hukumomi da aka fitar ranar Laraba suka nuna.

Gidan watsa labarai na kasar Isra'ila, KAN ya bayyana cewa wani sabon rahoto daga Cibiyar Bincike da Bayanan Majalisar Knesset ya nuna "bayanan damuwa game da ƙoƙarin kashe kai tsakanin sojojin Isra'ila."

Bayanan sun nuna ƙoƙarin kashe kai tsakanin watan Janairun 2024 zuwa Yulin 2025, inda aka lura cewa kashi 12 cikin 100 na waɗannan ƙoƙarin sun kasance masu tsanani sosai, kashi 88 cikin 100 matsakaita, sai kuma 36 daga cikinsu sun kai ga mutuwa.

A cewar rahoton, sojojin Isra'ila 124 sun mutu ta hanyar kashe kansu tun daga 2017 har zuwa Yulin 2025, inda kashi 68 cikin 100 ke cikin hidimar soja ta dole, kashi 21 cikin 100 suna dakarun ko-ta-kwana sai kuma kashi 11 cikin 100 suna kan aiki na dindindin.

Rahoton ya nuna karuwar yawan kashe-kashe tsakanin sojojin ko-ta-kwana tun daga 2023, yana danganta wannan da karuwar yawan sojojin da ke aiki tun bayan barkewar yaƙin Gaza.

“Annobar kashe kai, wadda ake tsammanin za ta ƙaru bayan ƙarshen yaƙin, tana buƙatar kafa ingantattun tsarin tallafi ga sojoji, aiki don kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe, da cim ma zaman lafiya na gaskiya,” in ji Ofer Cassif, mamba a jam’iyyar Hadash-Ta’al mai sassaucin ra’ayi.

“Gwamnatin da ke tura sojojinta zuwa yaƙi kuma ta bar su da matsalolinsu su kadai to ba ta son su ne,” in ji Cassif, wanda ya nemi a shirya rahoton.

Isra’ila ta kashe fiye da mutum 68,500, yawancinsu mata da yara, kuma ta jikkata fiye da 170,000 a hare-haren da ta kai a Gaza tun watan Oktoba 2023.

Yaƙin mai tsanani ya tsaya karkashin wata yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba karkashin shirin Shugaban Amurka Donald Trump mai ajanda 20.