| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Ghana ta lashe Kofin Duniya na kwallon kafar guragu
A hanyar lashe kofin, Ghana ta lallasa Amurka da ci 3-1 a zagayen 'yan-16.
Ghana ta lashe Kofin Duniya na kwallon kafar guragu
Nasarar ta mayar da Ghana ƙasa ta biyu a Afirka da ta lashe gasar. / Hoto: Ghana FA/Instagram / Others
 

A karon farko tawagar ƙwallon ƙafar guragu ta Ghana, “Black Challenge”, ta lashe Kofin Duniya na Ƙwallon Ƙafar Guragu, bayan ta doke Morocco da ci 1-0 ranar Lahadi a wasan ƙarshe da suka buga a Mexico.

Kyaftin ɗin tawagar, Richard Opentil shi ne ya ci ƙwallon da ta ba su nasara a minti na 32, a wasan ƙarshe da aka buga a filin wasa na San Juan de los Lagos.

Nasarar ta mayar da Ghana ƙasa ta biyu a Afirka da ta lashe gasar, bayan Angola ta lashe a 2018.

Haka nan, wannan ne karon farko da ƙasashen Afirka biyu suka buga wasan ƙarshe na gasar, inda Ghana ta ƙara jaddada fifikonta kan Morocco a manyan gasanni.

A baya ma ɓangarorin biyu sun taɓa haɗuwa a wasan ƙarshe na Kofin Afirka na Nakasassu a 2024, da kuma a gasar Wasannin Nakasassu ta Afirka, a 2023, inda a duka lokutan Ghana ta yi nasara.

A hanyar lashe kofin, Ghana ta lallasa Amurka da ci 3-1 a zagayen 'yan-16, da kuma nasarar ci 2-0 kan Masar a zagayen kwata-fainal.

Haka kuma, sun fitar da ƙasar da ke riƙe da kofin, wato Türkiye, da ci 4-3 a bugun fenareti a zagayen sami-fainal bayan wasan ya ƙare da ci 1-1 duk da ƙarin lokaci.

Ɗanwasan gaba na tawagar Ghana, Mubarik Mohammed ya lashe takalmin zinari na gasar bayan cin mafi yawan ƙwallaye, da ƙwallo bakwai.

Nasarar ta zamo wani babban matsayi ga harkar wasanni a Ghana, kuma tana ƙarfafa matsayin ƙasar a fagen ƙwallon ƙafar guragu da ke haɓaka.