Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ƙaddamar da Tsarin Tattalin Arzikin Halal na Ƙasa, wanda ke da nufin bai wa Nijeriya damar cin gajiyar kasuwar halal ta duniya wadda aka ƙiyasta darajarta ta kai dala tiriliyan 7.7, tare da faɗaɗa tattalin arzikin ƙasar.
Shugaban ƙasar, wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilta a wajen ƙaddamarwar da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ya ce wannan tsari na nuna shirye-shiryen Nijeriya na shiga cikin kasuwar halal ta duniya da ke ci gaba da bunƙasa.
Ya ƙara da cewa ana sa ran wannan shiri zai ƙara kusan dala biliyan 1.5 ga tattalin arzikin Nijeriya nan da shekarar 2027.
Tinubu ya bayyana cewa tsarin zai mayar da hankali kan faɗaɗa fitar da abinci mai bin ƙa’idar halal, bunƙasa masana’antar magunguna da kayan kwalliya, inganta yawon buɗe ido na halal, da kuma samar da hanyoyin kuɗi masu ɗa’a.
Ya ƙara da cewa ana sa ran wannan shiri zai samar da darajar tattalin arziki da ta haura dala biliyan 12 nan da shekarar 2030, tare da ƙarfafa samar da abinci da dama ga ƙananan da matsakaitan ‘yan kasuwa.
Da yake mayar da martani kan damuwar da ake danganta halal da addini kawai, Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima ya bayyana cewa tattalin arzikin halal yanzu ya zama tsarin kasuwa na duniya wanda ya fi mayar da hankali kan inganci, tsaro, bin diddigi, da samar da kayayyaki cikin gaskiya, ba wai addini kawai ba.
Ya kuma bayyana cewa ƙasashe da dama masu ci gaba kamar Birtaniya, Amurka, Canada, da Australia suna daga cikin manyan ƙasashen da ke taka muhimmiyar rawa a kasuwar halal.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa wannan tsari na cikin manufofinta na faɗaɗa fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje, jawo masu zuba jari na ƙasashen waje, da samar da ayyukan yi masu ɗorewa a faɗin ƙasar.













