Daga Noureldein Ghanem
Morocco ta fara azamar karɓar baƙuncin Gasar Kofin Ƙasashen Afirka karo na 34 daga 21 ga Disamba zuwa 18 ga Janairun 2026, inda ƙasashe 24 za su fafata don neman ɗaga kofin AFCON 2025.
Zagayen rukuni na gasar ya ƙunshi rukunoni 6, Rukunin A, wanda ya haɗa mai masaukin baƙi, Morocco, Mali, Zambia, da Comoros. Rukunin B yana ɗauke da Masar, Afirka ta Kudu, Angola, da Zimbabwe.
Rukunin C akwai Nijeriya, Tunisia, Uganda, da Tanzania. Rukunin D na da Kamaru, Ivory Coast (mai riƙe da kofi), Gabon da Mozambique.
Rukunin E: Algeria, Senegal, DR Congo, Burkina Faso; sai kuma a ƙarshe Rukunin F: Equatorial Guinea, Ghana, Benin, da Botswana.
Duk da cewa gasar ta haɗo sanannun tawagogi, AFCON gasa ce da ta yi ƙaurin suna wajen ba da mamaki, inda ƙasashen da ba a zaton nasararsu sukan yunƙuro su kayar da manyan ƙasashe a fagen ƙwallo.
Ga jadawalin tawagogin da ke da kyakkyawar damar lashe kofin, tare da sauran da za su gwada sa’arsu:
Tawagogin da ke da fifikon damar cin kofin:
Morocco
A matsayinta na mai masaukin baƙi, Morocco za ta buga gasar a matsayin wadda ake ganin tana cikin jerin masu takarar lashe kofin.
Duk da cewa tawagar ta Lions of Atlas ta samu cancantar shiga gasar kai-tsaye saboda karɓar baƙi, amma sun shiga wasannin neman cancanta, inda suka lashe duka wasanninsu takwas kuma suka ci ƙwallo 22 inda aka ci su sau biyu kacal.
Duk da akwai yiwuwar rashin zuwan ɗanwasan PSG, Achraf Hakimi saboda jinya, tawagar tana da manyan ‘yanwasa ciki har da Noussair Mazraoui na Manchester United, da Neil El Aynaoui na Roma, da Brahim Diaz na Real Madrid, da Youssef En-Nesyri na Fenerbahce da sauransu.
Kasancewar za su buga gasar a gidansu wata dama ce ga Morocco ta samu ƙarin ƙarfin-gwiwa, sakamakon tarin masoya da za su ƙara musu karsashi.
Tawagar ba ta faye tsaya wa kan salon wasa guda ba, amma tana yawan fita fili da zubin 4-3-3, inda takan daidaita tsakanin tsaron gida da kai farmaki, tare da bai wa ‘yanwasan gefe damar su iya kai hari.
Tawagar ta Morocco a yanzu tana matsayi na 11 a ƙwazo a fannin ƙwallo a Jerin FIFA.
Senegal
Duk da cewa Senegal tana yawan ƙoƙari a gasannin AFCON, sau ɗaya suka taɓa lashe kofin a 2021 bayan doke Masar a bugun fanareti a wasan ƙarshe.
A wannan karon, tawagar ta Lions of Teranga za ta gasar da fatan lashe ta a karo na biyu, inda take da su Sadio Mane na Al Nassr, da Nicolas Jackson na Bayern Munich, da Ismail Sarr na Crystal Palace, da Iliman Ndiaye na Everton.
Senegal takan yi zubin ‘yanwasa na 4-2-3-1, inda za ta dogara kan fannoni kamar ƙarfin tuwo da sauri da kuzari.
Senegal tana mataki na 19 a jerin FIFA rankings, inda mafi girman matakin da suka taka shi ne matsayi na 17.
Ivory Coast (Masu riƙe da kofi)
Ivory Coast ta samu nasara mai ban mamaki a wasan ƙarshe na gasar 2024, bayan da suka ci ƙwallo a ƙarshe-ƙarshen wasan, inda tawagar ta Elephants ta doke ta Nijeriya da ci 2-1.
A yanzu suna wani ɓangare ne na shirye-shiryen sake cin kofin kamar yadda suka yi a gasar da suka ɗauki nauyi.
Tawagar ta yi kusa da a fitar da ita tun a zagayen rukuni, inda da ƙyar ta tsallaka cikin tawagogin da suka zo na uku a rukuninsu.
A matakin rukunin, an kori kocin tawagar ana tsaka da gasar saboda raunin ƙwazo inda aka naɗa kocin riƙo.
Ivory Coast ba za a iya ture ta gefe ba, duk da dai tawagar ba a yawan saka ta a matsayin wadda ake ganin za su lashe gasar.
Duk da ƙungiyar ba ta kai ƙarfin lokacin da take da su Didier Drogba da Yaya Toure ba, Ivory Coast tana cikin wadda ta fi tara mafi tsadar ‘yanwasa a gasar, inda suka kai jimillar euro miliyan €291.43.
Masar
Masar ta daɗe da kafa tarihin zama mafi samun nasara a Afirka, inda take da kofuna 7. Amma bayan nasararsu a 2010, tawagar ta Pharaohs ta samu kanta a matsaloli a lokaci guda.
Masar ta gamu da ƙalubalen ƙauracewar ‘yanwasa, lokacin da tarin ‘yanwasa daga tawagarsu ta "Mafi Tagomashi" wadda ta yi tashe a Afirka daga 1998 zuwa 2010 suka yi ritaya.
Sai dai kuma, tawagar ta Masar ta farfaɗo cikin sauri, inda ta samu shiga gasar AFCON a 2017 har ta je wasan ƙarshe a 2017 da 2021.
Mutane na ganin babbar damar Masar ta maido da matsayinta na karagar ƙwallon Afirka, yayin da take da Mohamed Salah na Liverpool, da Omar Marmoush na Manchester City, waɗanda suke jan akalar Pharaohs.
Tawagar Masar ta yi suna wajen zubin ‘yanwasa, inda suke buga wasa na riƙe ƙwallo sannu-sannu, inda suke dogaro kan mai da hari da salon bi daki-daki idan suka rasa ƙwallo.
Masar tana matsayi na 34 a jadawalin taka ƙwallo na FIFA. Mafi girman matsayin da ta taka shi ne na 9.
Algeria
Tawagar Desert Warriors za ta je gasar AFCON tare da fatan lashe kofi a karo na uku bayan wanda suka lashe na ƙarshe a 2019.
A 2019, Algeria ta samu mafi kyawun jeranta yin nasara a wasa a tarihin ƙwallo, inda ta cika wasanni 35 ba tare da an doke ta ba. Equatorial Guinea ce ta kawo ƙarshen jarantawar a 2022.
Italiya ce kaɗai (da wasanni 37) da Argentina (mai wasanni 36) suka haura Algeria a buga wasanni a jere ba tare da rashin nasara ba.
Duk da cewa Algeria ba ta da zazzafar tawaga irin ta 2019, a yanzu za ta dogara kan ‘yanwasanta masu ƙwarewa waɗanda za su iya kai ta gaci.
Algeria tana matsayi na 35 a halin yanzu a jadawalin FIFA, inda mafi girman matsayin da ta kai shi ne na 15.
Kamaru
Wata ƙasar da ke da ƙarfi a fagen ƙwallo a Afirka ita ce Kamaru, wadda ta lashe kofin AFCON a karo na ƙarshe a 2017, bayan doke Masar da ci 2-1 a wasan ƙarshe.
Tawagar mai suna Untamed Lions sun saba zuwa gasar, saboda sun lashe gasar sau 5, inda Masar ce kawai ta ke samanta da kofuna 7.
Kamaru ƙasa ce da ta samar da tarin taurari da ke buga ƙwallo a manyan gasannin Turai guda biyar, kuma tana yawan taka rawar gani a gasar Afirka.
A wannan karon Kamaru na da Carlos Baleba na Brighton, Bryan Mbuemo na Manchester United, tare da sauran tsaffin hannu irinsu Vincent Aboubakar da Choupo-Moting da ke jan ragama.
Idan Kamaru ta yi nasara za ta kai su dab da matakin Masar a yawan kofuna. Masar ta riƙe wannan kambin na yawan kofuna tsawon kusan shekaru 20, tun sanda ta wuce Kamaru a 2006.
Ghana, wadda ta ci kofin sau huɗu, ba za ta halarci gasar ba a bana, shi ya sa Kamaru take da babbar damar karɓe karagar Afirka.
Nijeriya
Tawagar Nijeriya, wadda ake kira da Super Eagles, tana da babbar damar lashe kofin na AFCON a wannan shekara.
Tamkar Kamaru, Nijeriya ta yi suna wajen zaratan ‘yanwasa a manyan gasannin Turai.
A wannan AFCON ɗin, Nijeriya tana da tawagar da ta ƙunshi Calvin Bassey da Alex Iwobi na Fulham, da ‘yanwasan gaba zarata irinsu Ademola Lookman na Atalanta, Tolu Arokodare na Wolves, da gwarzo Victor Osimhen na Galatasaray.
Nijeriya tana da kofunan AFCON har uku, kuma ita ce ƙasar da ta fi kowacce a Afirka wajen taka matsayi mafi girma a jadawalin ƙwarewa a ƙwallo na FIFA, inda ta kai ta 5 a 1994.
Tawagogin da za a sa wa ido
Mali
Mali ba ta da kofin AFCON ko guda duk da ta zo ta biyu a 1972.
Cikin karo 14 na zuwanta gasannin AFCON, Mali ta samu kyautar tagulla sau biyu a 2012 da 2013, kuma ta zo ta huɗu har sau uku, a 1994, 2002 da 2004.
Don haka, zai zama banbaraƙwai a sako Mali cikin waɗanda za su iya lashe kofin bana, amma dai tawagar ta yi rawar gani a wasannin shar-fagen fara AFCON, inda ta ci wasanni huɗu ta yi canjaras biyu.
Tawagar ta Mali tana da matasan ‘yanwasa, kuma ‘yanwasanta uku ne kacal cikin 27 suka haura shekara 30. ‘Yanwasan suna da matsakaicin shekaru 26.
Tunisia
Tunisia ba kanwar lasa ba ne a gasar AFCON, saboda sun yi suna wajen samar da ‘yanwasa da ba da mamaki wajen doke manyan ƙasashe.
Ƙasar ta lashe kofin sau guda a 2004, inda ta lallasa Morocco da ci 2-1 a wasan ƙarshe.
A wani wasansu na sada-zumunta na ƙarshe tare da Brazil, Tunisia ta yi canjaras da ci 1-1. Wannan alamar kyakkyawan shirin gasar ne sama da wasu ƙasashen da za su buga AFCON.
Tunisia tana matsayi na 40 a jarin FIFA wajen ƙwarewa a ƙwallo.
Tawagar za ta dogara kan salon wasanta da ake wa laƙabi da na arewacin Afrika, wanda ya ƙunshi ƙaƙƙarfa tsaron gida, da saurin kai farmaki.
Afirka ta Kudu
Afrika ta Kudu ta ci kofin Afirka sau ɗaya kacal, amma tamkar Tunisia, tana da tarihin ba da mamaki da kai ƙatti ƙasa a gasannin baya.
Tawagar ta taka rawar gani a wasannin neman cancantar shiga gasar, inda ta ci wasanni huɗu ta yi canjaras sau biyu.
Tawaga mai tsauri ɗaya ce Afirka ta Kudu za ta fuskanta a rukunin, wato Masar, kuma masoyansu da dama suna da fatan zuwa na ɗaya a rukunin.
Afirka ta Kudu tana matsayi na 61 a jadawalin da FIFA ta fitar na ƙarshe.




















