| Hausa
SIYASA
2 minti karatu
An daƙile harin RSF kan West Kordofan: Rundunar Sojin Sudan
Rundunar sojin Sudan ta zargi RSF da kai hare-hare kullum kan Babnousa, wani birnin da aka yi wa ƙawanya na tsawon shekara biyu.
An daƙile harin RSF kan West Kordofan: Rundunar Sojin Sudan
Sojin Sudan ta ce ta daƙile harin RSF kan birnin na jihar West Kordofan / Reuters
2 Disamba 2025

Rundunar sojin Sudan ta ce ta daƙile wani harin da dakarun Rapid Support Forces (RSF) suka kai birnin Babnousa na Jihar West Kordofan, a kudancin ƙasar.

A wata sanarwa da ya fitar ta shafin sada zumunta ranar Talata, wani mai magana da yawun sojin ƙasar ya zargi RSF da kai hari a Babnousa a ko wace rana da manyan bindigogi “da kuma jirage maras matuƙa,” duk da cewa ƙungiyar ‘yan tawayen ta ayyana tsagaita wuta da kanta a baya.

Dakarun sojin ƙasar sun “daƙile” wani sabon harin da aka ƙaddamar ranar Litinin, in ji mai magana da yawun sojin.

Ɗakin ko-ta-kwana na Babnousa, wani kwamitin agaji na birnin, ya ce kimanin mazauna birnin 177,000 sun tsere daga birnin domin hare-haren bamabamai na RSF kan Babnousa, wanda ya kasance ƙarƙashin ƙawanya fiye da shekara biyu.

Rundunar sojin tana ganin shelar tsagaita wutar da ƙungiyar ‘ya bindigar da ƙawayenta suka yi "ba komai ba ne dabara ta siyasa da ta kafafen watsa labarai domin sakaye yadda suke tafiya a fagen yaƙi."

Shugaban RSF Mohamed Hamdan Dagalo ya ayyana tsagaita wuta a Sudan ranar 24 ga watan Nuwamba duk da cewa dakarunsa suna faɗaɗa iko a jihohin Darfur da Kordofan kuma sun kai hare-hare kan fararen-hula.

Mai magana da yawun sojin ya tattabar da jajircewa wajen martaba dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa da kare fararen-hula da kuma taimaka wa aikin jinƙai, yana mai cewa “ba za su ƙyale ana amfani da yanayi na jinƙai domin sakaye motsin soji da ke munana rikicin ba.”

Ba a samu tsokaci nan-take daga RSF ba kan jawabin sojin.

Daga cikin jihohin Sudan guda 18, RSF tana iko da dukkan jihohi biyar na yankin Darfur da ke yammaci, idan banda wasu sassan arewacin North Darfur wanda kawo yanzu na ƙarƙashin ikon soji. Rundunar sojin kuwa tana riƙe da yawancin jihohi 13 da suka saura a kudu da arewa da gabashi da tsakiyar ƙasar ciki har da babban birnin, Khartoum.

Rikicin tsakanin sojin Sudan da RSF, wanda aka fara a watan Afrilun shekarar 2023, ya kashe aƙalla 40,000 mutane tare da raba mutum miliyan 12, in ji hukumar lafiya ta duniya.