Bayan sanar da ƙwace mulki da wasu sojoji suka yi a Jamhuriyar Benin a ranar Lahadi, fadar shugaban ƙasar ta ce har yanzu Shugaba Patrice Talon ne a kan mulki inda gwamnatin Benin ɗin ta ce sojojin da suka yi sanarwar suna da iko ne kawai da gidan talabijin ɗin ƙasar.
Talon, mai shekaru 67, tsohon ɗan kasuwa ne da ake kira “sarkin auduga na Cotonou”, ana sa ran zai mika mulki a watan Afrilu na shekara mai zuwa bayan shekaru 10 a kan mulki.
Yammacin Afirka ta sha fama da juyin mulki a 'yan shekarun nan, ciki har da makwabtanta a arewa, Nijar da Burkina Faso, haka kuma Mali, Guinea da, kwanan nan, Guinea-Bissau.
A safiyar Lahadi, sojojin da suka kira kan su “Kwamitin Soja na Sake Gina Ƙasa”, a wani jawabi a gidan talabijin na ƙasar sun ce sun tattauna sannan kuma sun yanke shawarar cire Mista Patrice Talon daga kan mulkin ƙasar.
'Ƙaramin gungu wanda ke da iko da gidan talabijin'
An katse siginar daga baya a safiyar.
Bayan ɗan lokaci daga sanarwar, wani na kusa da Talon ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa shugaban yana lafiya.
“Wannan wani gungu ne kawai wanda ke da iko da gidan talabijin kaɗai. Rundunar soja ta yau da kullum na ƙoƙarin dawo da iko. Birnin (Cotonou) da ƙasar gaba ɗaya suna cikin tsaro,” in ji su.
“Abin da ake jira shi ne lokaci kafin komai ya daidaita. Aikin tsabtace lamuran na tafiya da kyau.”
'An shawo kan lamarin'
Wata majiyar soji ta tabbatar da cewa an “shawo kan lamarin” kuma masu ƙoƙarin juyin mulki ba su ɗauke ƙwace fadar Talon ba ko kuma ofishinsa.
Ofishin Jakadancin Faransa a wani bayani a shafin X ya ce “an ji harbe-harbe a Camp Guezo” kusa da mazaunin shugaban a birnin tattalin arzikin ƙasar.
Ofishin jakadancin ya yi kira ga 'yan Faransa da su zauna cikin gidajensu saboda dalilan tsaro.
Wani ɗan jarida na AFP a Cotonou ya ce sojoji suna toshe hanyoyin zuwa fadar shugaban ƙasa da tashar talabijin ta gwamnati.
'Yunƙurin juyin mulki da dama a baya'
An kuma toshe hanyoyi zuwa wasu wurare da dama, ciki har da otel din Sofitel mai tauraro biyar a Cotonou da unguwannin da ke dauke da hukumomin ƙasa da ƙasa.
Amma ba a ruwaito an ga sojoji masu yawa a filin jirgin sama ko sauran birnin ba, kuma mazauna suna ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Tarihin siyasar Benin ya ga juyin mulki da yunkurin juyin mulki da dama tun bayan samun 'yancin kai daga Faransa a 1960.
Talon, wanda ya karbe mulki a 2016, zai cika wa'adin mulkinsa na biyu a 2026, mafi tsawon lokaci da kundin tsarin mulki ya yarda da shi.
















