| Hausa
SIYASA
2 minti karatu
Nijar ta ce ta fara kai uranium ɗinta kasuwar duniya
Haƙar uranium a Nijar na cikin muhimman batutuwan jayayya da ke tsakanin gwamnatin da ta amshi mulki a shekarar 2023 da kamfanin Orano, wanda gwamnatin Faransa ce ta mallaki kashi 90 cikin 100 nasa.
Nijar ta ce ta fara kai uranium ɗinta kasuwar duniya
Shugaban Nijar ya ce Nijar ta ɗauki matakin sayar da uranium ɗinta a kasuwar duniya cikin cikakken 'yanci / AFP
1 Disamba 2025

Gwamnatin ƙasar Nijar ta bayyana ranar Lahadi cewa ta fara shigar da uranium ɗin da kamfanin Somair mallakin Orano na Faransa, ya haƙo - kafin gwamnatin ta mayar da shi mallakin kasar- a kasuwar duniya.

Haƙar uranium a Nijar na cikin muhimman batutuwan jayayya da ke tsakanin gwamnatin da ta amshi mulki a shekarar 2023 da kamfanin Orano, wanda gwamnatin Faransa ce ta mallaki kashi 90 cikin 100 na kamfanin kuma ya shafe gomman shekaru yana juya akalar mahaƙan ma’adinan a Nijar.

An bayyana wannan labarin ne a gidan tabalijin na ƙasar Tele Sahel a wani rahoton da aka fitar da yammacin Lahadi inda wanda ya ambato kalaman shugabna ƙasar Janar Abdourahamane Tiani.

Rahoton ya ce Tiani ya kama abin da Nijar take da ‘yancin yi na juya akalar ma’adinanta ta hanyar sayarwa ga duk wanda yake son ya saya a ƙarƙashin dokar kasuwa, cikin cikakken ‘yanci.”

Ministan makamashin Rasha, Sergei Tsivilev, dai ya bayyana a watan Yuli cewa Moscow na son ta haƙi uranium a Nijar.

Tun lokacin da gwamnatin ta karɓi mulki a juyin mulkin shekarar 2023, Nijar ta koma ga Rasha, wadda ke da rumbum makaman nukiliya mafi girma a duniya, domin tallafa mata wajen yaƙar masu tayar da ƙayar baya da ke iƙirarin jihadi a ƙasar da ke Yammacin Afirka.

Kazalika ta juya wa tsohuwar uwar gijiyarta Faransa baya inda ta zarge ta da taimaka wa ‘yan a-ware.

A shekarar 2024, Nijar ta ƙwace kamfanin Orano kan muhimman mahaƙar ma’adinai uku nata a ƙasar: Somair da Cominak da kuma Imouraren, waɗanda ke da tarin uranium mafi yawa a duniya.

A hukumance dai kamfanin Orano na da kashi 60 cikin 100 na hannayen-jarin ƙananan kamfanonin, kuma ya shigar da wasu ƙararraki domin ya sake samun iko kan mahaƙar ma’adinan.

A shekarar 2022 dai Nijar ce ta samar da kimanin kashi ɗaya cikin huɗu na uranium da aka kai tashoshin nukiliyar Turai, bisa alƙalluma daga hukumar makamashin nukiliya ta Turai Euratom.