| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Adadin mutanen da suka mutu a hatsarin kwale-kwale a Bayelsa ya kai 29, yayin da ake kan aikin ceto
Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ne ya tabbatar da ƙarin adadin waɗanda suka mutu a ranar Lahadi, yayin ziyarar da mataimakin shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya kai jihar.
Adadin mutanen da suka mutu a hatsarin kwale-kwale a Bayelsa ya kai 29, yayin da ake kan aikin ceto
Adadin mutanen da suka mutu sakamakon hatsarin kwale-kwale a jihar Bayelsa da ke kudancin Nijeriya ya karu zuwa 29 / TRT Afrika Hausa
 

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon hatsarin kwale-kwale a Jihar Bayelsa da ke kudancin Nijeriya ya ƙaru zuwa 29, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da gano gawarwakin sauran waɗanda suka mutu.

Hatsarin ya auku ne a ranar Juma'a, 20 ga Nuwamba, 2026, kusa da garin Oweikorogha da ke Ƙaramar Hukumar Southern Ijaw, lokacin da wani kwale-kwale mai ɗauke da fasinjoji, wanda ya taso daga garin Ayama zuwa Ukubie domin halartar wani taron jana'iza, ya kife.

Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ne ya tabbatar da ƙarin adadin waɗanda suka mutu a ranar Lahadi a Yenegoa, yayin ziyarar da mataimakin shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya kai jihar.

Diri ya ce ba a kai ga tantance ainihin adadin waɗanda suka mutu ba, saboda har yanzu ba a gano kwale-kwalen da ya kife ba. Ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar wasu fasinjoji na maƙale a cikinsa.

Gwamnan ya ce binciken farko ya nuna cewa, da an bi ƙa'idojin tsaron ruwa, da akwai yiwuwar ƙauce wa hatsarin.

A cewarsa, rahotannin farko sun nuna cewa kwale-kwalen ba shi da ingancin da zai iya jigilar fasinjoji, haka kuma wurin da aka loda fasinjojin ba ya cikin wuraren da aka amince da su domin hawa jiragen ruwa.

Masu AlakaTRT Afrika - Kwale-kwale ya kife da masu zuwa jana’iza a Bayelsa, ana fargabar da dama sun mutu

Gwamnatin jihar na haɗa kai da hukumomin gwamnatin tarayya da jami'an tsaro,da kuma masu sa kai daga al'ummomin yankin domin gudanar da aikin ceto da gano wadanda suka mutu.

Diri ya kuma ce gwamnatin jihar ta dauki nauyin kuɗaɗen jinya da abincin wadanda suka tsira daga hatsarin da ke samun kulawa a asibitoci daban-daban a Bayelsa.

Tinubu ya yi alƙawarin ba da N250M ga iyalan wadanda hatsarin ya shafa

A ɓangare guda kuma, shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, ya amince da bayar da tallafin naira miliyan 250 ga iyalan waɗanda hatsarin ya shafa.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu ne ya sanar da tallafin a ranar Lahadi yayin ziyarar ta'aziyya da ya kai Bayelsa, inda ya isar da saƙon ta'aziyyar gwamnatin tarayya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

Haka kuma Shettima ya ce Tinubu ya umarci hukumomin gwamnatin tarayya da su haɗa kai da gwamnatin jihar wajen tallafa wa iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma ƙarfafa ayyukan kai ɗaukin gaggawa.

Kazalika ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya umarci Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da ta samar da tallafi ga wadanda hatsarin ya shafa.

Haka kuma, shugaban ya umarci ma'aikatar kula da harkokin tattalin arzikin ruwa da ta tabbatar da an aiwatar da dokokin kiyaye lafiyar fasinjoji a hanyoyin ruwa na cikin gida.

An kuma umarci Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) da ta sayo kwale-kwale domin inganta harkokin sufuri a al'ummomin da ke zaune a yankunan da ruwa ya mamaye.

A yayin ziyarar, mataimakin shugaban ƙasar ya gana da waɗanda suka tsira daga hatsarin da ke karɓar magani a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Kiwon Lafiya ta Bayelsa, tare da jajantawa iyalan waɗanda suka rasa 'yan’uwansu.

Ya bayyana lamarin a matsayin babban bala'i da ya shafi ƙasa baki ɗaya, yana mai jaddada cewa mutanen da ke amfani da hanyoyin ruwa wajen zirga-zirga sun cancanci samun irin kariyar tsaro da ake bai wa masu amfani da hanyoyin mota da jiragen sama.

Tuni dai gwamnatin jihar Bayelsa ta soma bincike kan musabbabin hatsarin, inda ake sa ran sakamakon binciken zai taimaka wajen ɗaukar matakan hana sake faruwar irin wannan lamari a gaba.

Wannan mummunan hatsari ya sake jawo hankalin jama'a kan batun tsaron fasinjoji a hanyoyin ruwa na Nijeriya, musamman a yankunan da kwale-kwale ke zama sufurin zirga-zirga.

 

Rumbun Labarai
Haraji: Nijeriya ta bai wa kamfanonin kirifto da na hada-hadar kuɗaɗen intanet wa’adin yin rajista
Atiku ya buƙaci a yi bincike mai zaman kansa kan tsarin AI na INEC gabanin zaɓen 2027 a Nijeriya
Bola Tinubu: 'Ɗan ƙwalisar' akanta da ya ɗaukaka zuwa matsayin Shugaban Ƙasa
NAFDAC ta ƙwace kwalaye 17 na alluran bilicin 'marasa' rajista a filin jirgin saman Kano
Hare-haren sama na sojojin Nijeriya sun kashe 'yanta'addan ISWAP 21 a Borno
ADC ta shigar da kara mai hujjoji 17 a kan INEC kan soke takarar Atiku ta 2027
Jami’an Kwastam na Nijeriya sun kai ziyarar aiki Nijar don ƙarin ilimi kan dabarun tsaro
Jonathan ya yi gargaɗi kan rikicin ƙabilanci da rashin haƙuri a siyasa gabanin zaɓen 2027 a Nijeriya
Nijeriya ta kama mutum takwas bisa zargin safarar hodar iblis zuwa Turai ta Hamadar Sahara
Nijeriya na dab da samar da ‘yansandan jiha yayin da majalisun jihohi 36 suka amince da shirin
Hukumar hana safarar mutane ta Nijeriya ta bankaɗo yunƙurin safarar mutane 1,508
Tinubu ya yi wa mutum 78 afuwa bayan kama su da laifin kai hari ga ayarin motocinsa a Abuja
Majalisar yaƙin neman zaɓen APC ta ƙaddamar da shirin samar da tsaro na Tinubu na shekaru biyar
Sojojin Nijeriya sun kashe 'yanta'adda takwas, sun kuɓutar da mutum 125 da aka yi garkuwa da su
‘Yanbindiga sun kashe wani babban mai bai wa gwamna shawara a Zamfara
Faɗa tsakanin 'yanbindiga da 'yan sa-kai ya yi ajalin mutum fiye da 50 Jihar Zamfara ta Nijeriya
Jihar Katsina ta kaddamar da jami'an kula da gandun daji fiye da 1,000 domin magance matsalar tsaro
INEC ta saka ranar 28 ga Nuwamba domin gudanar da zaben gwaji gabanin zaben Nijeriya na 2027
Atiku ya buƙaci Tinubu ya yi bayani kan matakan da yake ɗauka na kawo ƙarshen kashe-kashe a Nijeriya
Jami'an DSS a Nijeriya sun kama makamai da ake zargi an shiga da su Jihar Sokoto daga Nijar