| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Biranen Afirka 25 da Amurka za ta rufe ayyukan bayar da biza daga ranar 1 ga Agustan 2026
A tsakiyar watan Yulin 2026, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da dakatar da bayar da biza daga birane 25 a faɗin Afirka, inda tilas masu neman bizar su tafi wasu biranen a abin da Washington ta bayyana "cibiyoyin yanki."
Biranen Afirka 25 da Amurka za ta rufe ayyukan bayar da biza daga ranar 1 ga Agustan 2026
Amurka ta maida ayyukan sarrafa biza a biranen Afirka 25 zuwa wasu wuraren.
 

A tsakiyar watan Yulin 2026, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da dakatar da bayar da biza daga birane 25 a faɗin Afirka, inda tilas masu neman bizar su tafi wasu biranen a abin da Washington ta bayyana "cibiyoyin yanki."

A sanarwar da Ma'aikatar ta wallafa a ranar 15 ga Yuli, ta ce: "Daga 1 ga Agustan 2026, Ma'aikatar Harkokin Wajen za ta sake daidaita ayyukan biza na yau da kullum a cikin biranen da aka ambata guda 25."

Biranen da abin ya shafa sune: Antananarivo (Madagascar), Abuja (Niijeriya), Asmara (Eritrea), Bamako (Mali), Banjul (Gambia), Brazzaville (Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo), Bujumbura (Burundi), Conakry (Guinea), Cotonou (Benin), Durban (Afirka ta Kudu), Freetown (Sierra Leone), Gaborone (Botswana), Harare (Zimbabwe), Juba (Sudan ta Kudu), Libreville (Gabon), Lilongwe (Malawi), Lusaka (Zambia), Maputo (Mozambique), Maseru (Lesotho), Mbabane (Eswatini), N'Djamena (Chadi), Yamai (Nijar), Nouakchott (Murtaniya), Ouagadougou (Burkina Faso), da Windhoek (Namibiya).

Masu neman biza, waɗanda a da za su shigar da buƙatar izinin shiga ƙasar a ofisoshin jakadanci ko ƙananan ofisoshin jakadancin Amurka a waɗannan biranen, yanzu tilas su tafi wasu birane, ko ma wasu ƙasashe, domin ganawar neman biza.

Bisa ga sharuɗɗan Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka, TRT Afrika ta tattara sabbin cibiyoyin neman biza ga mutanen da abin ya shafa. Ga bayanan biranen da abin ya shafa da kuma sabbin biranen da za su maye gurbinsu a gabansu:

Antananarivo (Madagascar) — Johannesburg (Afirka ta Kudu)

Abuja (Nijeriya) — Legas (Nijeriya)

Asmara (Eritrea) — Kampala (Uganda)

Bamako (Mali) — Dakar (Senegal)

Banjul (Gambia) — Dakar (Senegal)

Brazzaville (Jamhuriyar Kongo) — Kinshasa (Kongo DRC)

Bujumbura (Burundi) — Kampala (Uganda)

Conakry (Guinea) — Dakar (Senegal)

Cotonou (Benin) — Lome (Togo)

Durban (Afirka ta Kudu) — Johannesburg (Afirka ta Kudu)

Freetown (Saliyo) — Monrovia (Laberiya)

Gaborone (Botswana) — Johannesburg (Afirka ta Kudu)

Harare (Zimbabwe) — Johannesburg, Cape Town (Afirka ta Kudu)

Juba (South Sudan) — Kampala (Uganda)

Libreville (Gabon) — Yaounde (Kamaru)

Lilongwe (Malawi) — Nairobi (Kenya)

Lusaka (Zambia) — Johannesburg (Afirka ta Kudu)

Maputo (Mozambique) — Johannesburg (Afirka ta Kudu)

Maseru (Lesotho) — Johannesburg (Afirka ta Kudu)

Mbabane (Eswatini) — Johannesburg (Afirka ta Kudu)

N'Djamena (Chadi) — Yaounde (Kamaru)

Yamai (Nijar) — Lome (Togo)

Nouakchott (Mauritania) — Dakar (Senegal)

Ouagadougou (Burkina Faso) — Lome (Togo)

Windhoek (Namibia) — Johannesburg, Cape Town (Afirka ta Kudu)

Ma'aikatar ta ce: "‘Yanƙasa da mazauna waɗannan ƙasashe da suke son neman bizar Amurka a ranar ko kafin 1 ga Agustan 2026, dole ne su nemi lokacin da za a gana da su, kuma su biya kuɗin biza da ake buƙata a wuraren bizar da aka tsara."

Sauran ayyukan ofisoshin jakadancin da ƙananan ofisoshin jakadancin za su ci gaba

Washington ta ce ta daidaita ayyukan bizar ne a Afirka da wasu yankuna na duniya a matsayin "wani ɓangare na dogon tsarin Ma'aikatar wanda ke ƙarfafa tsaron ƙasa ta hanyar inganta daidaitattun matakan bincike, da antancewa, da yanke hukunci, da kuma inganta ayyuka."

Rumbun Labarai
Tsawatarwar diflomasiyya da aka yi wa jakadan Nijeriya abu ne da aka gama batunsa: Afirka ta Kudu
Ghana ta ba da shawarar fara amfani da kuɗin ECO a matakai tsakanin ƙasashen ECOWAS da suka shirya
Sojojin Sudan sun sami ƙarin wurare a jihar West Kordofan yayin da mayaƙan RSF ke ja da baya
Shugaba Tiani na Nijar ya nada Aboubacar Issaka a matsayin sabon shugaban ’yansandan kasar
Ghana na samun tan 62 na sinadarin mercury a kowace shekara ta hanyoyin da ba su dace ba
Rundunar tsaron Nijar ta ƙwace makamai da ake zargin ana shirin kai wa Boko Haram a Diffa
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da gyaɗa zuwa ƙasashen waje
Sudan ta Kudu ta sake dage babban zaben kasar zuwa ranar 11 ga Fabrairun 2027
Amurka za ta sa ido sosai kan zaben shugaban kasar Nijeriya na watan Janairu - Jami’i
An kashe fararen-hula akalla 37 a wani harin kwanton-ɓauna a yammacin Jamhuriyar Nijar
An kashe aƙalla mutum 10 yayin da dakarun tsaron Guinea suka yi arangama da masu haƙar zinare
Ghana za ta kashe dala miliyan 200 kan shirya wa gina tashar makamashin nukiliya
Ghana ta kaddamar da sabuwar takardar kudi ta Cedi
Burhan na Sudan ya buƙaci a cire siyasa a rabon tallafin yaƙi da sauyin yanayi ga ƙasashe mara ƙarfi
Greenpeace ta gargaɗi Ghana kan barazanar shara sakamakon shigo da tsofaffin tufafi miliyan 1 a mako
Yadda El Niño ke sake haifar da ɓarkewar cutar Zazzaɓin Rift Valley a Gabashin Afirka
BAMEX 2026: An fara baje-kolin fasahar tsaro ta ƙasa da ƙasa a Mali
Kotu a DR Congo ta yanke wa sojoji 66 hukuncin kisa saboda 'ja da baya a fagen daga'
Kwale-kwale dauke da ‘yan ci-rani ya kife a kusa da Senegal, mutum 21 sun rasu, in ji hukumomi
An yanke wa jagoran ƙungiyar asiri a Kenya hukuncin ɗaurin shekara 200 kan kisan yara 190