| Hausa
AFIRKA
1 minti karatu
An kawar da mazan jiyan Kamaru yayin da majalisar dokokin ta zaɓi sabbin shugabanni
Zaɓen sabbin shuwagabannin ya nuna muhimmin sauyi na shekarun shuwagabbin a cikin majalisun da kundin tsarin mulki ya bai wa damar gadar Shugaba Paul Biya.
An kawar da mazan jiyan Kamaru yayin da majalisar dokokin ta zaɓi sabbin shugabanni
Sabbin shugabannin majalisar dokokin suna matsayin iya gadar Shugaba Paul Biya. / Reuters / Reuters
2 awanni baya

Majalisar dokokin Kamaru a ranar Talata ta zaɓi Theodore Datouo na jam’iyyar CPDM mai mulki a matsayin sabon shugabanta, kamar yadda kafar watsa labaran ƙasar CRTV ta ruwaito, lamarin da ya kawo ƙarshen jagorancin shekara 34 na shugaba mai barin gado Cavaye Yeguie Djibril, mai shekara 86.

Datouo, mai shekara 65, da Aboubakary Abdoulaye, mai shekara 64 -wani sarkin gargajiya mai ƙarfin faɗa a ji - an zaɓe su ne su jagoranci majalisar wakilai da majalisar dattawan ƙasar.

Abdoulaye ya gaji Marcel Niat Njifenji, mai shekara 91, a matsayin shugaban majalisar dattawa.

Naɗa sabbin shugabannin ya nuna muhimmin sauyi na shekarun shugabanni a cikin majalisun da kundin tsarin mulki ya bai wa damar gadar Shugaba Paul Biya.

Biya, mai shekara 93, shugaban ƙasar mafi yawan shekaru a duniya, ya lashe zaɓen wa’adi na takwas a kan karagar mulki a zaɓen da aka yi zargin tafka maguɗi a watan Oktoba.

Sake zaɓansa ya tsawaita mulkinsa na kusan shekara 44 kuma zai iya sa ya ci gaba da jagorantar ƙasar da ke samar da mai da koko a tsakiyar Afirka zuwa kusan shekaru 100 da haihuwa.