| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Manyan jami'an China sun tattauna da Ƙungiyar OIC a yanayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ƙara muni
Mataimakin shugaban ƙasar China da ministan harkokin wajen ƙasar sun gana da babban sakataren ƙungiyar haɗin kan ƙasashen musulmi ta OIC, inda suka yi kira da a samar da haɗin gwiwa a fannin tsaron yankin yayin da rikicin Amurka da Iran ke ƙara muni.
Manyan jami'an China sun tattauna da Ƙungiyar OIC a yanayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ƙara muni
Ministan harkokin wajen China ya yi jawabi a taron Lanting da ke birnin Beijing. / Reuters
26 Janairu 2026

Mataimakin shugaban ƙasar China da ministan harkokin wajen ƙasar sun tattaunawa da babban sakataren ƙungiyar haɗin kan ƙasashen musulmi 57 ta OIC a ranar Litinin, a cewar wata sanarwa ta ma'aikatar harkokin wajen China ta fitar kana kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya rawaito.

Tattaunawar da aka gudanar a babban birnin ƙasar China na Beijing ta zo ne a daidai lokacin da ake ƙara samun tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya bayan da wani jami'in Iran ya ce ƙasar za ta dauki mataki kan duk wani hari da aka kai mata "a matsayin yaki mai zafi a kanmu".

Wadannan kalamai sun biyo bayan furucin shugaban ƙasar Amurka Donald Trump na cewa Amurka ta aika ‘‘manyan jiragen ruwanta na soji’’ zuwa Iran, inda ya kara da cewa saboda ‘‘abin da ka iya zuwa ya dawo,’’ ya kuma gargaɗin Iran da kada ta kashe masu zanga-zanga ko ta sake shirinta na nukiliya.

Wani jami'in ƙasar Iran a yankin ya fada a ranar Lahadi cewa akalla mutane 5,000 ne suka mutu bayan zanga-zangar da aka yi kan matsalar tattalin arziki.

A tattaunawar ta ranar Litinin, Ministan Harkokin Wajen China Wang Yi ya yi kira da a samar da kawance ta tsaro a yankin tare da warware matsalolin siyasa, in ji ma'aikatar.

Jami'an Amurka sun ce wani jirgin mai ɗukar kaya da wasu jiragen yaki masu sarrafa kansu za su isa Gabas ta Tsakiya a cikin kwanaki masu zuwa.

A makon da ya wuce ne, China ta ƙauracewa shirin kafa "Hukumar Zaman Lafiya" don Gaza wanda Amurka ke jagoranta, tana mai nuna damuwa kan tsoma baki daga waje.

A maimakon haka, China ta ce za ta kare tsarin ƙasa da ƙasa tare da Majalisar Dinkin Duniya "a matsayin jigon da za ta sa a gaba", kwana guda bayan sanar da cewa an gayyace ta shiga "Hukumar Zaman Lafiya don Gaza" ta Trump.

Beijing ta buƙaci ta tsaya daga tsakiya, ta hanyar haɓaka tattaunawa da ci gaban tattalin arziki a matsayin jigo na inganta zaman lafiya da tsaro na yanki.

China ta jaddada hakan ne a shekarar 2023, lokacin da ta shiga tsakani wajen sulhunta rikici mai cike tarihi tsakanin Iran da Saudiyya - wani mataki da ake kallo a za mastayin wata babbar gudummawa wajen rage tashin hankali a yankin da kuma karfafa tsaron Gabas ta Tsakiya.