Fadar shugaban Nijeriya ta ce Shugaba Bola Tinubu yana cikin ƙoshin lafiya kuma yana iya yin aikinsa a ko ina ba sai a Abuja, babban birnin tarayyar ƙasar ba.
A wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu ya fitar ranar Lahadi, ya ce ana sa ran shugaban na Nijeriya zai koma ƙasar a wannan makon daga Faransa, bayan shafe makonni yana ƙasashen Turai domin yin hutun aiki na shekara-shekara.
Tinubu ya bar Nijeriya a ranar 30 ga watan Agusta domin hutun mako uku na shekarar, inda ya fara zuwa Landan sannan daga bisani ya wuce Paris, a cewar fadar shugaban ƙasar.
Shugaba Tinubu “yana hutunsa na shekara, wanda yake da cikakken ikon yin hakan. A wannan lokaci na fasahar sadarwa ta zamani, ba lallai sai ya kasance a Abuja da kansa ba domin gudanar da aikin da aka zabe shi ya yi a shekarar 2023,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.
Onanuga ya ce Tinubu ya halarci taruka da masu zuba jari a Faransa, ciki har da tattaunawar da ta shafi wani shirin gina tashar jiragen ruwa a Ogun, wadda aka ƙiyasta za ta kai dala biliyan bakwai.

Sau biyu fadar shugaban Nijeriya tana sanar da tsawaita hutun shugaban ƙasar lamarin da ya jawo suka daga 'yan adawa, musamman bayan da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya wakilci Nijeriya a taron babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 a New York a makon jiya.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma ɗantakarar shugaban Nijeriya na jam'iyyar African Democratic Congress(NDC), Atiku Abubakar, ya yi suka tare da tambaya kan ko Tinubu ya sanar da shugabannin Majalisar Dokokin Nijeriya a hukumance kafin tafiyarsa, yana mai kafa hujja da sashe na 145 na kundin tsarin mulkin ƙasar.
Shi ma ɗantakarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Nigeria Democratic Party (NDC), Peter Obi, ya soki matakin shugaban na yin hutunsa a Turai, tare da tambayar dalilin da ya sa bai yi hutun a cikin Nijeriya ba.
Sai dai a ɓangare guda, Fadar shugaban ƙasar ta kare rashin komawar Tinubu Nijeriya a lokacin da aka soma bayyanawa, tana mai cewa yana ci gaba da tuntuɓar jami'an gwamnati tare da jagorantar harkokin gwamnati duk da yana hutu.
Ta kuma ce Shettima na da cikakken ikon wakiltar shugaban ƙasar a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya.
Onanuga ya ce Tinubu zai koma Nijeriya a wannan makon domin halartar wasu shirye-shiryen bikin cika shekaru 66 da samun 'yancin kan ƙasar, da kuma halartar bikin nuna wani fim a Legas da aka shirya domin tunawa da marigayi Moshood Abiola.






















