Sojoji Isra’ila da suka hada da manyan hafsoshi 23 da ke bakin aiki sun mutu sakamakon kashe kansu tun farkon shekarar 2026, adadin da ya kasance mafi yawa da rundunar sojin kasar ta samu a cikin shekaru 16, kamar yadda jaridar Haaretz ta rawaito a ranar Litinin.
Jaridar ta ce wasu karin sojoji 17 da suka taba shiga yaki sun mutu sakamakon kashe kansu a wannan shekarar bayan sun bar aikin soja.
Rahoton ya kuma ambaci mutuwar wasu mutane shida da ke karbar kulawa a cibiyoyin gyaran lafiyar kwakwalwa, da kuma 'yan sandan Isra'ila biyar sakamakon kashe kansu.
Wadannan alkaluma na nuni da ci gaba da karuwar yawan mutanen da ke kashe kansu a tsakanin jami'an tsaro na Isra'ila tun bayan barkewar yakin Gaza da Isra'ila ke yi, wanda aka fara a watan Oktoban 2023.
A cikin shekaru goma kafin yakin, rundunar sojin Isra'ila ta samu matsakaicin adadi na mutum 12 da ke kashe kansu a duk shekara, kamar yadda Haaretz ta bayyana.
Bayanan rundunar sojin sun nuna cewa sojoji bakwai da ke bakin aiki ne suka mutu sakamakon kashe kansu tsakanin 7 ga Oktoba zuwa karshen shekarar 2023. Adadin ya karu zuwa 21 a shekarar 2024, sannan ya kai 22 a shekarar 2025.
Yossi Levi-Belz, shugaban Cibiyar Nazarin Kashe Kai da Radadin Zuciya a Jami'ar Haifa, ya yi gargadin cewa sojojin Isra'ila, musamman wadanda aka kira domin aikin soja na wucin gadi (reservists), da ke ci gaba da hidima a shekarar 2026 da shekaru masu zuwa, suna cikin rukunin mutanen da ke cikin hatsarin kashe kansu.
"Shekaru masu zuwa za su kasance masu matuƙar muhimmanci, kuma watakila za su kasance masu tsananin muni idan aka yi la'akari da yawan mutanen da za su mutu sakamakon kashe kansu," in ji shi.
A cewar rundunar sojin Isra'ila, cikin tsoffin sojoji 17 da suka mutu sakamakon kashe kansu a wannan shekarar, rundunar ta tantance cewa akwai yiwuwar alaƙa mai ƙarfi tsakanin mutuwar mutane 10 daga cikinsu da aikin soja da suka gudanar, yayin da har yanzu ake ci gaba da binciken wani lamari guda.
Rahoton ya ce mafi yawan sojojin Isra'ila da ke bakin aiki da suka mutu sakamakon kashe kansu a wannan shekarar ba su nemi kulawar kwararrun lafiyar kwakwalwa ba kafin mutuwarsu.
Tun daga watan Oktoban 2023, yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, wanda ake zargin ta da aikata kisan kiyashi a cikinsa, ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da 74,000 tare da jikkata fiye da 176,000, mafi yawansu mata da yara. Haka kuma, yakin ya lalata kusan kashi 90 cikin 100 na ababen more rayuwa na yankin.
Sojojin Isra'ila sun kuma shiga wasu rikice-rikicen soji a yankin cikin shekaru biyu da suka gabata, ciki har da na Iran. Haka kuma, sun kai hare-hare kan Lebanon, Yemen da Qatar, tare da ci gaba da kai hare-haren kutsawa ta kasa da luguden wuta kusan kullum a Syria.
Tsawon shekaru da dama, Isra'ila ta mamaye Falasdinu da wasu yankuna na Lebanon da Syria, inda take ci gaba da kin janyewa daga yankunan ko kuma amincewa da kafa kasa mai cin gashin kanta ta Falasdinawa, kamar yadda kudurorin Majalisar Dinkin Duniya masu alaka da batun suka tanada.













