| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
NNPC na tattaunawa da kamfanin China domin farfaɗo da matatun man Nijeriya
Ƙasar da ta fi samar da ɗanyen mai a Afrika tana neman yadda za ta farfado da matatun manta bayan shekaru na asara da rashin aiki yadda ya kamata.
NNPC na tattaunawa da kamfanin China domin farfaɗo da matatun man Nijeriya
Direbobi na jira a layin domin shan mai a wani gidan man NNPC a Abuja. / Reuters
5 Fabrairu 2026

Kamfanin man Nijeriya, NNPC tana tattaunawa da wani kamfanin China game da ɗaya daga cikin matatun man kamfanin ƙasar, kamar yadda shugaban kamfanin man ya bayyana ranar Laraba.

Shugaban kamfanin NNPC Bayo Ojulari ya ce kamfanin na neman masu gudanarwa ƙwararru a matsayin masu zuba jari wajen farfaɗo da matatun man ƙasar guda huɗu bayan shekaru na asara da rashin aiki yadda ya kamata.

Ya ce bincike na cikin gida da aka yi jim kaɗan bayan ya karɓi ragamar kamfanin a watan Afriilun da ya gabata ya nuna cewa matatun man suna tafka asara mai yawa da tsadar kuɗaɗen gudanarwa da kuma kashe kuɗi mai yawa kan ‘yan kwangila yayin da man da ake tacewa ya kasance kaɗan.

Kwamitin gudanarwa na NNPC ya amince da wata dabara ta kawo ƙwararru masu gudanar da matatun mai waɗanda ke da tabbatacciyar ƙwarewa maimakon ‘yan kwangila, in ji Ojulari, yana mai cewa kamfanin na cikin wata tattaunawa da ta yi nisa da wasu da ke son shiga harkar.

"Yanzu haka daga wani zama nake da ɗaya daga cikin waɗanda za su iya zuba jari," in ji Ojulari, ba tare da ba da suna ba.

"Za su ziyarci matatar gobe domin gani da ido. Wani kamfanin China ne da ke da ɗaya daga cikin matatar mai mafi girma a China."

Nijeriya ta shafe shekaru tana fama da ƙoƙarin gyara tsofaffin matatunta wadanda aikinsu ya yi ƙasa da abin da ya kamata su iya yi, lamarin da ya tilasta wa ƙasar da ta fi samar da ɗanyen mai a Afirka ta dogara kan shigar da tacaccen mai.

Gwamnatin na fatan cewa sabuwar alaƙa ta haɗin gwiwa za ta taimaka wajen kawo ƙarshen wannan matsalar.

Ojulari ya ce an dakatar da aiki a matatun domin ba da lokaci na gwada hanyoyin da ake da su na farfaɗo da su, lamarin da ke faruwa a lokacin da aka ƙaddamar da matatar man Dangote, abin da ya ba "dama" ta samar da mai a gida.

Ya ce NNPC ba za ta sayar da matatun man ba, amma za ta sallamar da wani ɓangare na hannayen jarinsu ga abokan hulɗa domin tabbatar da cewa matatun sun iya dogaro da kansu a ayyukansu.