Ma’aikatar tsaron Turkiyya ta ce an gano wani jirgi maras matuƙi da ba a san shi ba ya nufo sararin samaniyarta ta kan Bahar Aswad kuma an bibiye shi kamar yadda ake yi a tsare-tsaren tsaro.
Domin tabbatar da tsaron sararin samaniyarta, an tayar da jiragen yaƙin F-16 waɗanda ƙawancen NATO ta samar kuma ƙasar take juya akalarsu domin wani aiki na kasancewa cikin shiri, kamar yadda ma’aikatar ta bayyana a wata sanarwa ranar Litinin.
Daga baya ya bayyana cewa jirgin maras matuƙin yana tafiya ne babu jagora, kuma daga baya aka kakkaɓo shi a wani wuri mara hatsari da ke da nisa daga inda mutane ke zama domin kauce wa ko wane irin hatsari, in ji sanarwar .
Lamarin na zuwa ne cikin tashin hankali a yankin Bahar Aswad, inda Turkiyya ta yi gargaɗin kada a bar yaƙin da ake yi a Ukraine ya fantsama zuwa hanyar cinikayyar yankin.


















