| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Dakarun Nijeriya sun kama mai 'kai wa Boko Haram jirage marasa matuƙa'
Wata sanarwa da jami’in watsa labaran OPHK, Laftanar Kanal Sani Uba ya fitar, ta ce mayaƙan Boko Haram suna amfani da jirage marasa matuƙa da mutumin ke kai domin kai hare-haren ta'addanci.
Dakarun Nijeriya sun kama mai 'kai wa Boko Haram jirage marasa matuƙa'
An kama mai kai wa mayaƙan Boko Haram jirage masara matuƙa / Nigerian army
20 Fabrairu 2026

Dakarun haɗin gwiwa na Operation Hadinkai (OPHK) tare da ‘yan sa-kai sun yi nasarar kama wani mutum mai suna Dauda Usman Gubula mai shekara 64 yayin da yake ƙoƙarin kai wa ‘yan Boko Haram jirage marasa matuƙa.

Wata sanarwa da jami’in watsa labaran OPHK, Laftanar Kanal Sani Uba ya fitar, ta ce mayaƙan Boko Haram suna amfani da jirage marasa matuƙan ne domin kai hare-haren ta'addanci.

Sanarwar ta ce an kama mutumin ne a tashar mota ta Madagali da jirage marasa matuƙa guda biyu da kayan gyaransu da fawabank na sola guda 20.

Masu AlakaTRT Afrika - An kashe sojoji 8 a wani harin wata ƙungiya mai alaƙa da Daesh a arewa maso gabashin Nijeriya

Kazalika sanarwar ta ce dakarun sun kashe wani kwamandan ‘yanta’adda Abdullahi Mafa a wani kwanton-ɓauna da suka yi mishi kusa da kogin Visik inda suka same shi da bindiga ƙirar AK47 da ƙwanson harsasai da ke cike da harsasai.

Har wa yau Laftanar Kanar Sani Uba ya ce dakarun sun kama wani Ismail Muhammed mai shekara 28 wanda ke safarar kayayyaki ga ‘yanta’adda a Visik a ƙaramar hukumar Hong ta jihar Adamawa.

Abubuwan da aka ƙwace daga hannunsa sun haɗa da ƙwanson harsasai na bindiga ƙirar AK47 da wasu harsasai da wasu kayayyakin sojoji da sauransu.

Bugu da ƙari sanarwar ta bayyana cewa dakarun OPHK tare da ‘yan sa-kai sun daƙile aika-aikar masu tayar da ƙayar baya a Ngamdu, da ke jihar Borno, kuma sun kashe wani infoma na ‘yanta’adda da ke ƙoƙarin ƙeta shingen tsaro.